✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kashe-kashe: Shaikh Gumi ya bukaci Buhari ya yi murabus

Ya ce babu sauran uzurin da za a yi wa Buhari kan kashe mutane da ake yi kullum.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Shaikh Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus tunda ya kasa tsare rayukan al’umma.

Kiran Shaikh Gumi na zuwa ne bayan kisan gillar da ’yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno.

Malamin ya ce kashe-kashen da ake yi a Gwamnatin Buhari ya ninka na gwamnatin da ta gabata, don haka babu wani uzuri da za a ci gaba da yi wa gwamnatin.

Shaikh Ahmad Gumi ya koka kan yadda ya ce kullum rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba na salwanta saboda gazawar gwamnati mai ci.

Ya yi wannan kira ne a yayin da yake gabatar da wa’azi a masallacinsa da ke Kaduna.