✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe-kashe a makarantun Yobe

A kwanakin baya ne ’yan bindiga da aka hakikance sun kai kimanin 20, suka auka wa wata makarantar sakandaren kwana a kauyen Mamudo da ke…

A kwanakin baya ne ’yan bindiga da aka hakikance sun kai kimanin 20, suka auka wa wata makarantar sakandaren kwana a kauyen Mamudo da ke Jihar Yobe, inda suka shiga dakunan kwanan dalibai suka kewayen daliban da ke barci, suka rika jefa musu bama-bamai tare da bude musu wuta da bindigogi, inda suka kashe 42 ciki har da wasu malamansu.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma cinna wuta a wasu gine-ginen makarantar. Hari na Mamudo shi ne na uku irinsa tun daga ranar 14 watan Mayun bana, lokacin da Gwamnatin Tarayya ta ayyana kafa dokar ta-kaci a jihohin Yobe da Borno da Adamawa. An tura dubban sojoji zuwa jihohin uku domin magance hare-haren kungiyar Boko Haram.
A ranar 16 ga Yuni, ’yan bindiga sun bude wuta a wata makarantar sakandare a garin Damaturu, inda suka kashe dalibai bakwai da malamai biyu. Su ma maharan an kashe biyu daga cikinsu a cewar sojoji. Washegari kuma ’yan bindiga suka kashe dalibai tara lokacin da suka zauna domin rubuta jarrabawar kammala karatu a wata sakandare mai zaman kanta a Maiduguri. A baya kungiyar Boko Haram ta rika kai hare-hare ga makarantu, tana kone gine-ginensu, amma ba ta cika kai hari ga dalibai ba.  Ba a san manufar kai hare-hare na baya-bayan nan ga dalibai da malamai ba, duk da cewa falsafar kungiyar ya ginu ne kan karatun boko haram ne. Kuma shugaban kungiyar Abubakar Shekau a wani faifan bidiyo da aka aika ta intanet ya ce, kungiyar ‘ta goyi bayan’ harin na Mamudo, ba tare da daukar nauyin kashe-kashen kai-tsaye ba. “Muna ba da cikakken goyon baya game da kai harin a makarantar boko ta Mamudo, kamar yadda aka ruwaito shi a kaset din yana fada.
A wani kangare na dabarun sojoji na magance hare-haren, an katse tarho a dukkan jihohin uku da dokar ta-kacin ta shafa. Kan wannan dalili ne aka ruwaito Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam yana cewa, rashin kafar sadarwar ya taimaka wajen munin matsalar, yana mai cewa ya taimaka wajen mugun karnar da kisan mummuken na Mamudo. Gwamnan ya ce, mazauna kauyen wadanda suka ’yan bindigar suna iya sanar da sojojin randunar hadin gwiwa in da a ce tarho yana aiki.
Matsalar mai matukar daure kai ne a tsoma baki a ciki, saboda harshen damon da ke cikinta, hakika katse wayoyin tarho ya taimaka wajen gurgunta hare-haren da ake kaiwa da bama-bamai a jihohin da ake batu ciki har da Yobe. Wannan ne ya sa maharan suka canja salo zuwa ga kai hari ga inda ba za su sha wuyar cim musu ba, kamar makarantu.
Sakamakon wannan danyen aiki ne Gwamna Gaidam ya ba da umarnin a rufe dukkan makarantun da ke jihar, domin ba mahukunta lokaci su nemo hanyar da ta fi dacewa wajen kare rayukan dalibai da malamai. La’antar da ta biyo bayan wannan mugun aiki daga kowane kangare ta nuna adawa da wadanda suka aiwatar da ita. Kuma a fili yake cewa akwai bukatar hukuma ta nemo hanyar magance hakan; ba ta kame hannuwa don nuna babu abin da za ta iya yi a kai ba. Lamarin ya sa Shugaba Goodluck Jonathan ya nuna kacin ransa har da la’ana ga wadanda suka yi aika-aikar yana cewa, “Babu shakka makomarsu wuta.” Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) da Jama’atu Nasril Islam kuwa kira suka yi a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan kisan.
kasashe da dama ciki har da Kanada da Faransa da kungiyoyin kare hakkin dan Adama na gida da waje su ma sun la’anci kisan gillar, suna kiran a gudanar da gagarumin bincike. Sannan sojoji sun tura wani ayarin soja zuwa Mamudo domin bincikar lamarin. Yayin da da’awar gwamnati na kawo karshen hare-hare a Arewa maso Gabas, na iya zama gaskiya, abu ne mai ban mamaki kusan wata biyu da gagarumin aikin sojoji, maharan suna ci gaba da kai irin wannan mugun hari. Sojojin da aka tura a karkashin dokar ta-kaci bai kamata su tsaya ga amfani da karfi kadai don zakulo maharan ba, nemo bayanan sirri na da matukar muhimmanci, kuma hada kai da mazauna yankunan shi ne kashin bayan cimma nasara.
Yayin da rufe makarantun ya dace a yanzu, a tabbatar mataki ne na wucin-gadi domin a yi rigakafin aukuwar bala’i irin na Mamudo. Rufe makarantun na dogon lokaci zai dada karfafa gwiwar ’yan Boko Haram ne. A matsayin matakin rigakafi, wajibi ne gwamnati ta katange daukacin makarantu a matsayin karin tsaro kafin a sake bude su. Ya kamata Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Yobe su samar da tallafi ga iyalan dalibai da malaman da aka kashe a Mamudo da sauran yankuna tun daga lokacin da aka kafa dokar ta-kacin.