✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe-kashe a Binuwei- Majalisar Wakilai na neman Buhari

A yau Laraba ne Majalisar Wakilai ta aike wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da takardar gayyata a game da ci gaba da kasha-kashen da ya…

A yau Laraba ne Majalisar Wakilai ta aike wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da takardar gayyata a game da ci gaba da kasha-kashen da ya dabaibaye kasar nan.

 

Hakanan kuma majalisar ta amince da dage zamanta na kwana uku domin nuna alhininsu bisa yadda ake kashe ‘yan Najeriya ba gaira ba dalili.
Sannan kuma majalisar ta bukaci a kaddamar da masu kisan a matsayin ‘yan ta’adda, sannan kuma ayi wa makiyaya ragista. Sannan daga karshe majalisar ta bukaci kwamitin da ke alhakin a kan lamarin da ya bincika lamarin, sanna ya kawo rahoto.

An samu wannan matsaya ne bayan dan majalisa Mark Gbillah, dan jam’iyyar APC daga Jihar Binuwei ya bukaci hakan, bayan kisan gillar da aka yi malaman majami’a biyu da wasu mutune 17 a jihar a jiya Talata.