✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe dukiya saboda Allah

Huduba ta Farko: Godiya ta tabbata da Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan amintaccen bawanSa Annabi Muhammad da alayensa…

Huduba ta Farko:

Godiya ta tabbata da Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan amintaccen bawanSa Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba Shi da abokin tarayya a gare Shi, kuma na shaida shugabanmu Annabi Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa. Ya Allah Ka kara tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan jagoranmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ina yi wa kaina da kuma ku da jin tsoron Allah tare da gudanar da rayuwarmu kamar yadda Allah Ya umarce mu a cikin fadinSa: “Yaku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, kuma ku kasance tare da masu gaskiya.” (At-tauba: 119).
’Yan uwana maza da mata a cikin Musulunci, hudubarmu ta yau tana magana ne a kan ciyarwa a tafarkin Allah.
A yau akwai Musulmi da dama da suka dauka Allah bai bukatar komai daga gare su, don haka sai su ta bauta ta yau da kullum da ta mako ko wata ba tare da sun tsaya sun yi dogon tunani ba, kuma ba tare da sun sadaukar da komai na dukiyarsu domin amfanin jama’arsu da sauran wadanda suke cikin kunci ba. Irin wadannan Musulmi suna ganin cewa sallarsu da azuminsu da hajjinsu da umararsu kadai sun isa samar musu da yardar Allah tare da samun gidan Aljanna.
Wasu daga cikinsu imaninsu a baka yake, suna daukar kansu tsarkakakku, babban abin da suka fi jin dadin yi, shi ne mujadala kan kananan baututuwa suna kawo Alkur’ani da Hadisi. Damuwarsu ta ta’allaka kan kananan al’amura ta yadda suka yi watsi da manya kuma muhimman al’amuran da suke damun Musulmi a yau. Irin wadannan Musulmi su muke kira ‘Musulmin gado’ damuwarsu zahiri shiga ba hakikanin Musulunci ba.
Shin sun yi daidai? Shin wannan dabi’a ta wadatar? Shin Allah zai karbe mu a matsayin Musulmin gado? Shin za mu iya zama masu imani na hakika ta yin Sallah kawai kamar yadda muka saba ba tare da kula sosai ba?
A cikin Surar Bakara aya ta 177, Allah Yana cewa: “Bai zama addini ba, domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira da mala’iku da littattafan sama da annabawa, kuma ya bayar da dukiya a kan yana son ta ga mai zumunta da marayu da matalauta da matafiyi da masu roko, kuma a cikin fansar wuya (’yanta baiwa), kuma ya tsayar da Sallah kuma ya bayar da zakka da masu cika alkawari idan sun kulla alkawarin da masu hakuri a cikin tsanani da cuta da lokacin yaki. Wadannan su ne suka yi gaskiya. Kuma wadannan su ne masu takawa.”
A cikin aya daya mai karfafa zuciya an gaya mana balo-balo me ‘addini na gaskiya’ yake nufi. Musulmi nagari bas hi ne wanda yake kawai fuskantar gabas ko yamma yana Sallah ba. A’a shi ne wanda daukacin rayuwarsa ya sadaukar da ita wajen bauta ga Allah da hidima ga bayin ko halittun Allah. Mumini na gaskiya zuciyarsa cike take da tsoron Allah da takawa da girmama Allah da tsarkake Shi. Wadannan su ne siffofin Muttaki, wato wanda zuciyarsa kecike da takawa (tsoron Allah).
 ’Yan uwa maza da mata, wajibi ne mu yi imani imani na gaskiya cewa Allah Ya koyar da mu ta cikin littattafanSa da manzanninSa, don haka yana da muhimmanci mu yi aiki da wannan imani. Mu nuna imanin a aikace, idan babu aiki babu manufar imanin namu. Ba za mu raba sauke hakkin Allah da kuma hakkin jama’a ba. Saboda haka ne ma za mu iske a wurare akalla 18 inda Alkur’ani Mai girma yake cewa: “Akimsus salata, wa atu zakkata.” Ma’ana “Ku tsayar da Sallah, kuma ku ba da zakka (sadaka)”.
daya hakki ne na Allah, dayar kuma hakki ne da muke mika shi ga ’yan uwamu mutane. Kuma duk da cewa su biyun suna karfafa juna ne, yin Sallah ba tare da bayar da zakka tamkar baya-ba-zane ne. Sannan bayar da zakka ba domin Allah ba, zai zamo ya kauce wa manufa kuma ba za a samu sakamako a kai ba. Mu bayar da zakka ko sadaka bisa jin dadi da son Allah ba domin wani dalili na daban ba, kamar riya da neman suna ko burge mutane. Bayar da sadaka ta farilla wato Zakka da ta wajibi kamar zakkar fidda-kai da kuma ta nafila kamar sadakoki wajibi ne su kasance an yi su domin nuna godiya ga Allah da neman lada daga Allah.
Tilas mu kasance masu tunatar da kanmu cewa duk yadda muka kai da ilimi ko dukiya ko samun nasara a wani al’amari, mun shigo wannan duniya ce ba mu da komai, kuma za mu bar ta mu tafi ba tare da komai ba, face abin da muka aikata a duniya (mai kyau da mara kyau). Kashe dukiya ta hanyar da Allah Yake so, muna nuna masa so ne muna bin umarninSa.
Babu wani dalili na halittarmu face domin mu bauta wa Allah da kyautata wa halittunSa, ya alla mu malamai ne ko ’yan  kasuwa ko ’yan siyasa ko ma’aikatanngwamnati ko na kamfanoni ko leburori da sauransu. To ina batunwadanda da gangan suka ki kashe dukiyarsu ko amfani da lokacinsu ko kwarewa da fasaharsu ko karfi da matsayi da mukaminsu wajen yin abin da Allah Yake so? Sun kunshi zumbuli masu kankamo da dukiyarsu kuma marowata. Me Alkur’ani ya ce game da su?
A aya ta karshe ta Suratu Muhammad ko kitali an gargade mu kan son zuciya da son kai da rowa inda aka ce duk ayyukan Shaidan ne: “Ga ku, ya ku wadannan! Ana kiranku domin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa’an nan daga cikinku akwai mai yin rowa. Kuma wanda yake yin rowa, to yana yin rowa ne ga kansa. Kuma Allah ne Wadatacce alhali kuwa ku fakirai ne. Kuma ida kuka juya (daga yi masa da’a), zai musanya wadansu mutane, wadansunku, sa’an nan ba za su kasance kwantankwacinku ba.” (k:47:38).
A fili yake Allah ba Ya son masu son zuciya. Son zuciya kuma na nuna rashin yarda da rashin imani da rahamar Allah. Mutane masu son kai ko son zuciya sukan nuna cewa suna tanadi ne wa kansu domin kauce wa shiga tsanani da bukata. Ashe ba Allah ne Mafi alherin masu kariya ba? Ina son zuciyarsu ya cutar da ruhinsu, kuma matukar ba su koma wa gaskiya ba, Allah ba za su samu karfin imani ba. Kuma rashin imaninsu ne yake sa Shaidan samun galaba a kansu wajen hana su aikata aikin alheri da dukiyarsu kamar yadda yake cikin aya ta 268 a Suratu Bakara: “Shaidan yana yi muku alkawarin talauci, kuma yana umartar ku da alfasha, kuma Allah Yana yi muku alkawarin gafara daga gare Shi da falala, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.” (k:2:268).
Khalin Jibran ya ce: “Ba tsoron kishi ba ne, lokacin da rijiyarka ke cike, a’a kishi ne da ba a iya magance shi.”
’Yan uwa maza da mata! Ya kamata mu rika lura da Shaidan da hanyoyinsa n araba mu da imani. Idan muka yi himma bisa ikhlasi, Allah zai karfafa imani a zukatanmu ta yadda tsoron talauci ba zai hana mu ciyar da matalauta ko ciyar da dukiya saboda Allah ba. An yi mana alkawari a cikin Alkur’ani cewa: “Ba za ku samu kyautatawa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, ko mene ne, to, lallai ne Allah gare shi, Masani ne.” (k:3:92).