Ƙasashe bakwai ne suka faɗa a ƙarƙashin mulkin soji cikin shekaru uku a Afirka bayan a shekarun 2000 nahiyar ta yi bakwana da juyin mulki, inda a wasu lokuta sukan kai ga zubar da jini.
Ga jerin ƙasashen da ke ƙarƙashin sojoji a nahiyar daga shekarar 2020 zuwa yanzu.
- Mali
- Chadi
- Guinea
- Sudan
- Burkina Faso
- Nijar
- Gabon
1- Mali
Juyin mulki na farko a daga shekarar 2020 shi ne wanda sojojin Mali suka yi a cikin watan Agusta, inda Kanar Assimi Goita ya kifar da da gwamnatin Shugaban Ibrahim Boubacar Keita, ya miƙa mulkin ƙasar ga Kanar Bah Ndaw (mai ritaya) a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.
Daga baya Kanar Assimi ya kifar da shi a wani sabon juyin mulkin a watan Mayu 2021, ya naɗa kansa a matsayin sabon shugaban riƙon kwarya.
2- Chadi
A watan Afrilun 2021 sojoji suka ci gaba da mulki a ƙasar Chadi bayan rasuwa Shugaba Idriss Deby Itno a fagen yaƙi da ’yan tawaye.
Bayan rasuwarsa ne ɗansa, Janar Mahamat Idriss Deby ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar ƙarƙashin mulkin riƙon ƙwarya, wanda wasu ke gani a matsayin juyin mulki a cikin ruwan sanyi.
3- Guinea
A watan Satumban 2021 Kanar Mamady Doumbouya ya jagoranci sojoji suka yi wa Shugaban Alpha Code na ƙasar Guinea juyin mulki.
Sojojin sun hamɓarar da Alpha Conde ne shekara guda bayan ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar domin ba shi ikon kara wa’adin mulki.
4- Sudan
A ranar 25 ga Octoban 2021, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ja jagoranci sojoji suka ƙwace gwamnati a juyin mulkin da suka yi bisa zargin rikicin ’yan siyasa da ya jefa ƙasar cikin rikici.
4- Burkina Faso
Kafin Nijar sai da sojoji suka yi juyin mulki sau biyu a Burkina Faso inda a watan Janairun 2022 Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba ya kifar da Gwamnatin Roch Kabore kan zargin gaza yaƙar ta’addancin da ya addabi ƙasar.
Bayan wata tara a watan Satumba, Kyaftin Ibrahim Traore ya yi masa juyin mulki ya ƙwace iko da ƙasar.
6- Nijar
Kafin nan a ranar 26 ga watan Yuli Sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki, lamarin da har zuwa yanzu da takwarorinsu an Gabon suka bi sahu ake ake ci gaba da kai ruwa rana wajen ganin sun saki Bazoum, sun miƙa masa kujerarsa, su koma bariki.
7- Gabon
An wayi garin Laraba 30 ga watan Agusta da labarin cewa sojojin Gabon sun hamɓarar da Shugaba Ali Bongo Odimba, sa’o’i kaɗan, suka soke zaɓen tare da rufe iyakokin ƙasar, suka kuma rushe duk masu rike da muƙaman siyasa.
Sojojin sun kifar da gwamnatinsa ne sa’o’i kaɗan ban ya lashe zabe domin fara wa’adinsa na uku a ƙaramar kasar mai arzikin mai da koko da sauransu.