✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kasar Thailand ta halasta noman Wiwi don magani

Sai dai ta yi gargadi kan sha a bainar jama’a

Kasar Thailand ta halasta noman Tabar Wiwi da mallakarta da kuma amfani da ita a cikin abinci da ababen sha.

Kasar ta dauki wannan mataki ne da zummar bunkasa fannin nomanta gami da harkokin yawon shakatawa, kuma ita ce kasa ta farko a nahiyar Asiya da ta dauki irin wannan matakin.

Sai dai, duk da halasta mu’amala da Wiwin da Thailand din ta yi, ba ta yarda a sha shi don nishadi a bainar jama’a ba saboda hakan ya saba wa dokar kasar.

Ya zuwa ranar Juma’a ake sa ran Ministan Lafiya na kasar, zai raba irin shukawa na Wiwin guda miliyan daya don karfafa wa manoman kasar nomanta.

A hannu guda, gwamnatin kasar ta ce, ta halasta noman tabar ce saboda dalilai da suka shafi kiwon lafiya.

Daga nan, ta yi gargadin shan wiwin a bainar jama’a cewa laifi ne wanda ka iya haifar da hukuncin dauri na wata uku da kuma tarar Dala 780, daidai da 25,000 na kudin kasar.