Tawagar kasar Kamaru da ake yi wa lakabi da The Indomitable Lions, ta fara da kafar dama a wasanta na farko wanda ta bude gasar Kofin Nahiyyar Afirka na AFCON 2021, inda ta yi nasara da ci 2-1.
Kamaru ta shige gaban Burkina Faso a zagayen farko na wasansu a gasar da suke bude a yau Lahadi, 9 ga watan Janairun 2022.
- Kar a yi la’akari da jam’iyya ko addini a Zaben 2023 —Sanusi II
- Gobara: Gwamnati za ta tallafa wa ’yan kasuwar Nguru
Bayanai sun ce shugaban kasar Kamaru, Paul Biya da Samuel Etoo, sabon shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kamaru suna cikin wadanda suka kalli wasan da aka fafata a filin wasanni na Paul Biya da ke Olembe a Yaounde, babban birnin kasar.
A dai-dai minti na 25 ne dan wasan tsakiyar Burkina Faso, Gustavo Sangare na Kungiyar Al-Nassr ya jefa kwallon farkon a raga bayan kwarbar da aka sha a yadi na goma sha takwas na bangaren gidan Kamaru.
Mintuna 3 kafin tafiya hutun rabin lokaci ne Kamaru ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda a nan dan wasan tsakiyarta Aboubakar wanda shi ke mata goma da kaftin ya zare kwallon.
Daf da za a tafi hutun rabin lokacin ne dan wasan baya na Burkina Faso, Nouhou Tolo ya yi wa Issoufou Dayo na Kamaru keta a raga, lamarin da ya sa alkalin wasa ya sake ba su bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma Aboubakar bai yi wata- wata ba ya sanya kasarsa Kamaru a gaba.
A haka aka nade tabarmar nishadin da sakamakon wasan a 2-1, lamarin da ya bai wa Kamaru damar darewa teburin rukunin A na gasar.
A halin yanzu Burkina Faso ce a kasan teburin rukunin A, inda kasashen biyu za su buga wasansu na gaba a ranar 13 ga watan Janairu.
A wasanninsu na gaba, Kamaru wadda ita ce mai masaukin baki a gasar za ta fafata da Ethiopia (Habasha), yayin da ita kuma Burkina Faso za ta barje gumi da Cape Verde.