✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasar Girka ta ba wa Najeriya tallafin rigakafin COVID-19

Kasar ta Greece ta bada tallafin ne don ci gaba da yaki da COVID-19 a Najeriya.

Kasar Girka ta ba wa Najeriya tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19  na kamfanin Johnson and Johnson guda miliyan daya.

Ministan Harkokin Waje na Girka, Nikolaos Dendias ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin wata ganawa da jami’an gwamnatin Najeriya a Abuja.

Dendias ya ce sun ba wa Najeriya tallafin rigakafin allurar ne da zimmar karfafa mata gwiwa kan yaki da ta ke yi da cutar.

Gwamnatin Tarayya na ci gaba da karbar tallafin allurar rigakafin COVID-19 daga kasashen duniya, amma ta yi gargadi cewa ba za ta sake karbar rigakafin da ya kusa lalacewa ba.

Ko a watan Disamba sai dai Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta lalata allurar rigakafin COVID-19 guda miliyan daya da suka lalace.

Kazalika, Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jan hankalin ’yan Najeriya wajen muhimmancin karbar rigakafin cutar, don kare kai da kuma ’yan uwa daga kamuwa da cutar coronavirus.