✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin kudin shekarar 2018 ya kai Triliyan 8.6

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya shiya gabatar da Naira triliyan 8.6 a matsayin kasafin kudin badi. Wannan kasafin, idan har aka tabbatar da shi, zai…

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya shiya gabatar da Naira triliyan 8.6 a matsayin kasafin kudin badi.

Wannan kasafin, idan har aka tabbatar da shi, zai zama cewa an samu karin kashi 15 ke nan a kan kasafin bara, wanda aka yi na kimanin Naira triliyan 7.44.

Amma dai za a iya samun sauye-sauye a kasafin kudin daga shugaban qasar, ko kuma majalisa. Sannan kuma Gwamnatin Tarayya ta ce za ta gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa a watan Oktoba.

Shi dai wannan kasafin kudin, an shirya shi ne a kan zaton cewa za a riqa sayar da gangan mai a Dala 45, sannan kuma za a riqa haqo ganga miliyan 2.51 a kullum. Sannan kuma canjin Dala, a Naira 305 akan kowace Dalar Amurka.