✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin Kudin Badi ya tasar wa Naira tiriliyan 7

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da tsarin kasafin kudin badi na Naira tiriliyan shida da biliyan 900, wanda ke nuni da karin Naira tiriliyan…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da tsarin kasafin kudin badi na Naira tiriliyan shida da biliyan 900, wanda ke nuni da karin Naira tiriliyan daya a kan kasafin kudin bana, wanda aka yi na Naira tiriliyan shida da biliyan shida (N6.06 tr).
Fasalin kasafin kudin yana kunshe ne a cikin wani kundi da ke dauke da bayanan yadda za a kashe kudin a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2019 (MTEF) da takardar da ke bayanin kan tsarin hada-hadar sarrafa dukiya (FSP), wadanda Shugaban kasar ya aike wa Majalisar Dokoki ta kasa A ranar Talatar da ta gabata.
Ya aike da kundin bayanin ne ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.
Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen gabatar da kasafin kudin shekarar 2017. Kundin ya fayyace tsare-tsaren gwamnati na tattalin arziki da zamantakewa da manufofin bunkasa kasa, tare da dabarun da za abi wajen cin musu.
Shugaban kasar ya yi nuni da cewa faduwar darajar man fetur a tsaskiyar shekarar 2014 ta haifar da matsalar tattalin arziki ga Najeriya a cikin gida da waje.
An tsara kasafin ne kan farashin man fetur na Dala 42 kan kowace ganga a kasafin na badi maimakon Dala 38 a bana.
Kudin musaya sun tashi daga Naira 197 kan kowace Dala zuwa Naira 290, amma yawan gurvataccen man fetur da ake hakowa yana nan a kan miliyan biyu da dubu 200.
Za a kashe kudin hada-hadar yau da kullum na Naira tiriliyan biyu da biliyan 600; sai Naira tiriliyan guda da biliyan 800 don aiwatar da manyan ayyuka; da Naira tiriliyan daya da biliyan 600 don rage basussuka da kuma Naira biliyan 370 na kason da za a raba daga kudin shiga.
Kason kudin da aka ware don kawo dauki na Naira biliyan 350, wanda ya yi kasa da Naira biliyan 150 daga kason wannan shekarar na Naira biliyan 177, wanda aka tara a wani asusu don biyan basussuka.
Kasafin kudin ya yi nuni da cewa, akwai Naira tiriliyan biyu da biliyan 600 da aka ware don hada-hadar biyan bukatun yau da kullum da Naira tiriliyan daya da biliyan 800 don daukar dawainiyar ma’aikatan sassan ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Sauran su ne Naira biliyan 188 na fansho da Naira biliyan 180 da za a kashe da Naira biliyan 120 na fansho; da wasu Naira biliyan 145 da miliyan 700 kudin ayyuka da aka ware; da Naira biliyan 65 da aka ware na kudin afuwar Shugaban kasa da Naira biliyan 50 da za a mayar a asusun ajiya na musamman.
Tsarin hada-hadar kudin kasafin dai na shekara uku ne, wanda aka fasalta kamar haka:
Naira tiriliyan 6,866,335,052,740 – 2017.
Naira tiriliyan 6,847,573,238,276 – 2018.
Naira tiriliyan 7,117,671,597,899 – 2019.
Kundin ya yi bayanin yadda gwamnati za ta bude asusun Dala biliyan 25 don samar da  ababen more rayuwa, ta yadda za a samar da wasu kudin shiga na daban daga kasafin kudin.
Kundin ya kimanta yawan kudin shigar cikin gida (GDP) zai bunkasa da da kashi 3.02 cikin 100 a shekarar 2017. Sannan an kimanta bashin da ake bin kasar nan da Dala biliyan 61 da miliyan 450, wato kimanin Naira tiriliyan 16 da biliyan 300.