✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin 2024 na jihohin Najeriya 36

Jihohin Kudu suke daga matsayi na daya zuwa na bakwai wajen yawan kasafi, a Arewa kuwa jihar Kogi, wadde ke matsayi na takwa ita ce…

Ga jerin kudaden da jihohin Najeriya 36 suka ware a matsayin kasafin kowannensu na shekarar 2024.

Jerin na nuna daga jihar da ta kasafinta ya fi girma zuwa wadda nata ya fi kankanta.

Kasafin jihohin Kudu ne suka fi yawa, inda suke daga matsayi na daya har zuwa na bakwai (Ribas, Ogun, Kuros Riba, Legas, Akwa Ibom, Bayelsa da Imo).

Jihar Kogi wadda take a matsayi na takwas ita ta wadda kasafinta ya fi yawa daga Arewacin Najeriya da Naira biliyan 32.4, sai Zamfara mai biliyana 30.7 a matsayin ta biyu a Arewa, amma ta 11 a fadin Najeriya, sannan Borno.

Ga jerin kasafin johihi 36:

  1. Ribas — ₦147.8b
  2. Ogun — ₦63.7b
  3. Kuros Riba — ₦61.6b
  4. Legas — ₦57.5b
  5. Akwa Ibom — ₦49.4b
  6. Bayelsa — ₦39.4b
  7. Imo — ₦34.5b
  8. Kogi — ₦32.4b
  9. Oyo — ₦31.2b
  10. Delta — ₦30.9b
  11. Zamfara — ₦30.7b
  12. Abia — ₦27.3b
  13. Anambra — ₦25.4b
  14. Edo — ₦22.9b
  15. Adamawa — ₦18.8b
  16. Enugu — ₦18.4b
  17. Borno — ₦17.2b
  18. Ekiti — ₦16.1b
  19. Gombe — ₦14.9b
  20. Binuwe — ₦12.5b
  21. Nasarawa — ₦12.5b
  22. Ebonyi — ₦10.9b
  23. Kebbi — ₦10.3b
  24. Katsina — ₦10.3b
  25. Kano — ₦9.7b
  26. Ondo — ₦8.5b
  27. Taraba — ₦8.4b
  28. Neja — ₦6.9b
  29. Osun — ₦6.5b
  30. Filato — ₦6.3b
  31. Kaduna — ₦6b
  32. Jigawa — ₦4.2b
  33. Kwara — ₦4.2b
  34. Yobe — ₦4.1b
  35. Sakkwato — ₦3.7b
  36. Bauchi — ₦2.9b

Alkaluma; Statista.