Majalisar Wakilai ta bukaci a kara wa bangaren tsaro bayan wanda aka ware masa a kasafin 2021.
Shugaban Kwamitin Majalisar kan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Abdulrazak Namdaz ya ce biliyan N840.56 da aka ware wa bangaren daga cikin Naira tiriliyan 13.08 na kasafin 2021 ba za su iya sayen makamai da gudanar da ayyukan samar da tsaro a sassan kasar ba.
- Abuwan da ke cikin kasafin 2021 na Najeriya
- Buhari ya mika wa Majalisa kasafin 2021
- Dokar mai: Majalisa za ta yi mahawara 20 ga Oktoba
Da yake kira a bullo da hanyoyin samar da kudaden tsaro baya ga kasafin kudi, Namdas ya ce, “Mu jingine ware wa bangaren tsaro kudade daga kasafin kudi; Babu kasar da ke amfani da kasafinta wajen biyan bukatun bangaren.
“Na san gwamantin na bayar da abin da za ta iya ne kuma ba za ta ba bangaren dukkannin kudadenta ba saboda sauran bangarorin ma suna bukata.
“Ba ina nufin cewa abin da ake ware wa bangaren ba daidai ba ne. Akwai kudurin dokar da aka yi wa karatu na biyu a Majalisar da ke jiran karatu na uku” inji shi
Idan ba a manta ba Majalisar Wakilai ta kammala karatu na biyu kan kudurin dokar kafa “Asusun Tallafa wa Rundunar Sojin Najeriya” wanda Honorabul Babajimi Benson da wasu mutum shida suka gabatar.