Mai tsawatarwar Majalisar Wakilai Mohammed Tahir Monguno ya bukaci bangaren zartarwa ya ware karin kudade ga bangaren noma a kasafin badi a matsayin noma na kashin bayan tattalin arzikin Najeriya.
Honorabul Monguno ya kuma bukaci a ware karin kudade domin farfado da tsaro ta abubuwan jin dadin rayuwa a yankin Arewa maso Gabas mai fama da matsalar tsaro.
- Majalisa za ta yi wa kasafin 2021 karatu na biyu
- Kasafin 2021: Majalisa ta bukaci a kara wa bangaren tsaro kudi
- Gwamnatin Bauchi ta dage dakatarwar da ta yi wa Sarkin Misau
Monguno ya ce kara wa yankin Arewa maso Gabas kudade a kasafin ya zama wajibi idan aka yi la’akari da irin barnar da rikicin Boko Haram ya yi wa abubuwan more rayuwa a yankin.
Dan Majalisar ya ce yin hakan shi ne matakin farko na farfado da yanayin abubuwan more rayuwa a yankin da ya shafe sama da shekara 11 yana fama da rikicin Boko Haram.
Yayin tsokacinsa a lokacin karatu na farko da majalisar ta yi wa kasafin na tiriliyan N13.08 Monguno da ke wakiltar mazabar Marte/Monguno/Nganzai ya ce a gwamnatocin baya sun yi wa yankin kwange a kasafin kudi.
Ya kuma bukaci gwamnati da ya mayar da hankali wajen bunkasa bangaren noma, wanda ya ce ke samar da kashi 70 na ayyukan yi a Najeriya da ma kasashen Afirka.