An tsinto gawar akalla mutum 25 bayan kasa ta rufta da masu hakar zinari a kudancin Nijar, kamar yadda dan majalisar yankin ya shaida wa BBC.
Masu aikin ceto da mutanen yankin na amfani da hannu da wasu kayan aikin hakar rami domin ceto masu sauran kwana yawancin matasa da dama da kasa ta rufta da su a kauyen Kondago.
- Wahalar man fetur ta mamaye birnin Kano
- Kotu ta daure Abdulrasheed Maina shekara 61 kan badakalar fansho
Shaidun gani da ido sun ce kokarin da ake na ceto rayukan ya gamu da cikas na rashin kayan aikin da suka dace a kauyen.
Rahotanni sun ce kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa ruftawar kasar ba.
Tun samun zinari a yankin Maradi a farkon shekarar nan, daruruwan mutane ke tururuwa zuwa yankin domin samo arzikin zinari.
Karo na biyu ke nan da kasa ta rufta da masu hakar zinari a Maradi inda mutum takwas suka mutu.