Wasu masana harkar lafiya a Kano sun ce ya kamata gwamnatin tarayya da ta jiha su sanar da al’umma hakikanin abin da ke faruwa dangane da karuwar mace-macen da aka samu a birnin a baya-bayan nan.
Da yake mayar da martani ga kalaman jagoran tawagar gwamnatin tarayya da ta je ba da tallafi da kuma taimakawa wajen binciken sanadin mace-macen, Farfesa Usman Yusuf, wanda kwararren likitan jinni da bargo ne kuma tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), ya nuna gamsuwa da bayanan da ya ji.
Jagoran tawagar dai, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, ya shaida wa manema labarai cewa sakamakon bincike na farko-farko ya nuna cewa COVID=19 ce ta haddasa da dama daga cikin mace-macen.
- COVID-19 ce dalilin mace-macen Kano —Dokta Gwarzo
- Yawaitar mace-mace: Kwankwaso ya nemi Buhari ya kai dauki
“Gwamnati ta fito ta sanar da alumma gaskiyar lamari. Kowa yana sane da irin dimbin mutanen da ke mutuwa a kullum wanda kuma yake karuwa.
“Na sha fadi cewa mace-macen nan na da alaka da wannan cuta. Idan Gwamnati ta ci gaba da boyewa to mutane suna cikin hadari.
“Sanar da su shi zai sa mutane su fadaka su rika takatsantsan tare da bin duk wasu matakan kariya sau da kafa. Idan kuma ba haka ba to muna ji muna gani wannan cuta za ta zo ta kashe mu”, inji Farfesa Yusuf.
‘Ba don an rufe gari ba…’
Masanin ya kuma musanta batun cewa wai don an rufe Kano ne ake mace-macen
“Kafin a kulle Kano sai da aka fara rufe Legas da Ogun, to su.me ya sa ba a yi wadannan mace-macen a can ba?”
Dokta Nasir Sani Gwarzo dai ya ce rufe iyakoki da aka yi da hana zirga-zirga sun sanya samun kai majinyata asibiti ya dan yi wahala, lamarin da ya sa wadanda ke da kwantattun cututtuka suka rasa kulawar da suke bukata a kan lokaci.
Farfesa Yusuf ya kuma yi kira ga al’umma da su bayar da gudummawarsu wajen yakar wannan annoba.
“Yakin nan ba na gwamnati ba ne ita kadai. Gaskiya sai kowa a cikinmu ya sanya hannu da duk wata hanya da yake da ita don fatattakar wamnan cuta”, inji shi
Aminiya ta zanta da wasu mazauna birnin Kano a kan yadda suke kallon wannan lamari.
Akwai alaka
Dokta Yusuf Kofar Mata ya bayyana cewa duk da yake kai-tsaye ba za a ce coronavirus ce ta haifar da yawan mace-macen ba amma yawanci suna da alaka da barkewar annobar.
“Idan mun duba bangarorin kula da lafiya na musamman a kukkule suke, saboda haka masu fama da cututtika daban-daban ba su da damar ganin likita.
“Haka kuma a yanzu haka an ce ba a aiki sosai a sashen gaggawa na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano saboda rashin isassun kayan aiki, a irin wannan yanayi an kawo mutane cututtukansu sun tashi yaya za a yi da su?
“Ai sai wanda yake da tsawon kwana ne kadai zai tsallake. Kai wasu ma za su iya mutuwa saboda fargabar cutar ko kuma wasu masu son addini ne wadanda ba su fahimci maganganun malamai ba su shiga damuwa saboda ba a zuwa masallachi da sauransu.”
‘Talauci ma ya taka rawa’
Ita ma Malama Nafisa Sani cewa ta “wasu, musamman masu hali, sukan je kasashen waje don a duba lafiyarsu amma a yanzu babu halin tafiya—wannan ma kadai ya isa ya kawo wadannan mace-mace. Haka ma talauci sakamakon kullen da ake yi shi ma wani dalili ne na mace-macen.”
Sai dai a ra’ayin Hamza Aminu Baba, akwai alaka a tsakanin karuwar mace-macen da cutar coronavirus.
“Mace-macen nan annoba ce wacce ko ba a fadi ba tana da alaka da cutar coronavirus, saboda yawancin mutanen da ke mutuwa tsofaffi ne wadanda kuma kowa ya san ba su da garkuwar jiki mai karfi. Kuma ko a Turai cutar ta fi hallaka tsofaffi”, inji shi.
Karuwar mace-macen dai, wadda ba a tabbatar da dalilinta ba, ta jefa al’ummar Kano cikin rudani, lamarin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ayyana dokar hana fita kwata-kwata ta mako biyu ya kuma aike da tawagar masana don yi bincike a kan lamarin.
A yanzu haka kuma alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta najeriya (NCDC) nan una cewa jihar Kano ce ta biyu a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.