✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

KAROTA za ta dauki karin ma’aikata

Hukumar KAROTA za ta dauki karin jami'ai da za ta tura zuwa sabbin masarautun Jihar Kano.

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) za ta dauki sabbin ma’aikata 700, dominkara wa jami’ai 2,500 da take da su a Jihar karfi.

Manajan Daraktan Hukumar, Baffa Dan’agundi, ya za a tura sabbin jami’an ne su yi aiki a sabbin masarautun  Bichi, Gaya, Karaye da Rano domin tabbatar da kiyaye dokokin ababen hawa.

Dan’agundi ya kuma gargadi ‘yan talla da ke neman dawowa kan tituna da sauran wuraren da aka haramta yin hakan a birnijn Kano.

“Mun tsananta domin ganin ‘yan tallan da aka tayar ba sake dawowa suna haddasa wa masu amfani da tituna matsala ba”, inji shi.

A cewarsa, nan gaba hukumarsa za ta yi hadin gwiwa da Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar Kano (KARMA) domin gyaran tituna da ke cikin birnin Kano da kewaye.