Hukumar KAROTA a Jihar Kano ta cafke jabu da kuma lalatattun magunguna na kimanin naira miliyan 30.
KAROTA ta yi wannan wawan kamun ne a ranar Alhamis bayan jami’anta da ke lura da Tashar Kano Line da kuma Titin Zariya sun samu wasu bayanan sirri dangane da motar da ta dauko dakon miyagun kwayoyin.
- Rikicin Nijar: Ba kasashen Yamma muke yi wa amshin shata ba — ECOWAS
- Za mu dauki fansar dakarun da aka kashe a Neja — Rundunar Soji
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar K/Na’isa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Juma’ar.
A cewarsa, jami’an na KAROTA sun cafke direban motar dauke da takardun shaidar daukan dakon kaya da sauyawa kwanan wata, lamarin da ya jefa musu ayar tambaya suka shiga bincike.
Nabilusi ya ce a yayin binciken ne suka gano cewar duk magungunan da direban ya dauko na jabu ne da kuma wadanda suka lalace sakamakon cikar wa’adin amfani da su.
Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin magungunan da aka samu har da magungunan kashe kwari.
Sauran kuma sun hada da magungunan ciwon ciki, kashe radadi, amoxicillin, allurar diclofenac, ciprofloxacin, paracetamol, dexamethasone da sauransu.
Manajan Darakta na KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya alakanta wannan nasara da sabon tsarin tumke damarar jami’ai da hukumar ta shimfida.
Ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da lura kan ire-iren wadannan magunguna na jabu da ka iya zama sanadiyar ajali ko kuma yi wa lafiyarsu mummunan lahani.