✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kebbi ta Tsakiya: Zaben Sanata da zai fi na gwamna Zafi

Karon batta tsakanin tsohon Gwamnan Kebbi, Adamu Aliero da Gwamna Atiku Bagudu kan Kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya a 2023

Bisa dukkan alamu karon batta mafi zafi da za a yi a zaben 2023 a Jihar Kebbi shi ne na Sanatan Kebbi ta Tsakiya.

Ana hasashen ko zaben gwamnan jihar ba zai yi zafi kamar na Sanatan Kebbi ta Tsakiya ba, bisa la’akari da karfi da kuma gogewar siyasa da kuma farin jinin ’yan takarar da ke neman kujerar.

Zaben da ke tafe a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, za a fafata ne tsakanin gwamnan mai ci, Sanata Atiku Bagudu na Jam’iyyar APC da tsohon gwamna kuma Sanata mai ci, Adamu Aliero.

Hasali ma, an fara cukumurdar siyasa tsakanin manyan ’yan siyasan, wadanda a baya dukkaninsu ’yan Jam’iyyar APC mai mulkin jihar, tun kafin zaben dan takararta na kujerar.

Cuku-cukun siyasa

Watanni kadan kafin zaben dan takarar, manyan ’yan siyasar jihar kuma ’yan a-mutun Aliero, suka sauya sheka zuwa PDP, suka jira komawar uban gidan nasu, bayan alamu sun bayyana cewa hakarsa ba za ta cimma ruwa ba a APC.

Masu sauya shekar a lokacin sun hada da tsohon tsohon Maitaimakin Sakataren Yada Labaran APC, Sani Dododo; tsohon Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Samaila Abdulmumini Kamba; da tsohon Shugaban jam’iyyar na jihar, Bala Sani Kangiwa.

Sauran su ne tsohon Daraktan Kamfe na Dan Takarar Gwamnan Jam’yyar APC, Farouk Marshall; Mataimakin Shugaban Yankin  Kudancin Kebbi na Jam’iyyar, Atiku Alaramma; takwaransa na Kebbi ta Kudu da sauransu.

Kwanakin kalilan kafin zaben dan takarar Sanatan Kebbi ta Tsakiya na APC ne Sanata Aliero ya aike wa Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, takardar janyewarsa daga zaben, tare da zargin ana masa rashin adalci a jam’iyyar duk kuwa da irin sadaukarwar da yake mata a matakin jiha da ma kasa.

Daga baya ne ya gudanar wani taron magoya baya da mukarrabansa, inda ya sanar da sauya shekarsa zuwa PDP, tare da aniyarsa ta komawa kujerarsa ta Sanata a karkashin inuwar jam’iyyar tasa.

An ja layi

Daga nan ne aka ja layi tsakaninsa da Gwamna Bagudu da shi ma yake neman kujerar bayan karewar wa’adinsa na biyu a 2023.

Duk da haka, a jawabinsa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben dan takarar, Bagudu ya ce takarar tasa ba ta a-mutu-ko-a-yi-rai ba ce.

Ya kuma nuna takaicinsa bisa sauya shekarar Aliero zuwa PDP, amma ya ce hakan ba barazana ba ce ga nasarar APC a zaben da ke tafe.

A cewarsa, “Na taba janye wa Sanata Aliero bayan na lashe zaben dan takarar Sanata, yanzu ma zan iya yin hakan domin samun zaman lafiya da ci gaban jam’iyyarmu a Jihar Kebbi.”

Sai dai kuma, bakin alkalami ya riga ya bushe, kasancewar Aliero ya riga ya sauya sheka zuwa PDP, inda yake kalubalantar gwamnan da ke neman maye gurbinsa a kujerar ta Kebbi ta Tsakiya.

Zaben zai yi zafi

Masu lura da harkokin siyasa ke ganin za a yi kare jini, biri jina a zaben da za a fafata tsakanin manyan ’yan takarar biyu a 2023.

Hasali ma, ana hasasehn ba zaben gwamnan jihar na 2023 ba zai kai na mazabar zafi ne, duba da fice da kuma yawan magoya bayan kowanne daga cikin ’yan takarar.

Wani hadimin Gwamna Bagudu, Alhaji Farouk Musa Yaro Enabo, ya bayyana cewa sun yi hadin gwiwa da manyan ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da ’yan PDP don tabbatar da ganin Bagudu ya kai bantensa.

Rundunar yakin zaben Bagudu

Shi dai Alhaji Farouk Musa Yaro Enabo, ana kallon sa a matsayin mutum daya tamkar da rundunar siyasa kuma gogaggen mai tsara dabarun siyasa na APC a jihar.

Bayan shi akwai irin manyan ’yan siyasa da ke da ke fadi-tashin nema wa gwamnan goyon baya a burinsa na zama Sanatan Kebbi ta Arewa.

Daga cikinsu akwai irinsu su Alhaji Farouk Kuru, Alhaji Ibrahim Bagudu, Alhaji Abubakar Nayaya da Alhaji Sani Sauro daga kananan hukumomin takwas da ke mazabar — Jega, Kalgo, Bunza, Gwandu, Maiyama, Birnin Kebbi, Aliero da kuma Koko Besse.

Za a yi karon batta

Wani mai lura da harkokin siyasar jihar ya ce, “Za a ci kwakwa a zaben domin Aliero ya kama kasa kuma ya shirya, haka ma Gwamna Bagudu.

“Bagudu zai iya samun goyon bayan manoma da masu sana’ar hannu da direbobi da masunta da ’yan tireda da masu kananan sana’o’i saboda sun amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa.

“Tsare-tsaren noma da gwamnatinsa ta yi, musamman shirin tallafin Anchor Borrowers na iya sa manoma a fadin kananan hukumomi takwas da ke mazaber su zabi Sanata Bagudu,” in ji shi.

Ya kara da cewa, ’yan majalisar dokokin jiha da kwamishinoni da mashawarta da shugabannin kananan hukumomi da kusoshin jam’iyya a fadin jihar suna tare da gwamnan kuma za su taimaka masa wajen ganin ya ci zabe.

Aliero zai koma cikin sauki

A daya hannun kuma, magoya bayan Aliero irin su Sakataren Yada Labaran PDP na jihar a yanzu, Alhaji Sani Dododo, na ganin uban gidansu zai sake komawa kujerarsa cikin ruwan sanyi kamar yadda ya saba.

“A matsayinsa na tsohon gwamnan daga 1999 zuwa 2007, Aliero ya kafa ’yan siyasa kuma har yanzu shi ke jya akalarsu. Manyan ’yan siyasa da dama shi za su yi.

“Tsohon gwamna ne kuma tsohon minista sannan sanata mai ci tun 2015, sannan nasarorinsa na siyasa a bayyane suke a fadin jihar nan.

“Idan ka lura yawancin manyan ’yan siyasa masu fada a ji a matakin gunduma da mazabu suna tare da shi.

“Shi ne kadai dan siyasa a Kebbi da zai iya kiran duk wani dan siyasa a kowacce daga kananan hukumoin jihar 21 ya nemi wani abu a wurinsu, kuma su yi.”

Yaransa ne

“Akasarin ’yan bokon jihar PDP suke yi kuma yaransa ne sannan sun karu da shi a lokacin da yake gwamna, ko yake minista ko yanzu da yake Sanata.

“Zaben zai zama lokacin da za su mayar masa biki kuma mtuanensa a kananan hukumomi a shirye suke su tara masa kuri’u a kananan hukumomin mazabar.

“Daga 1999 zuwa yanzu shi kadai ne ya yi gwamna sannna ya ci gaba da tallafa wa jama’a da rancen yin  sana’o’i.

“Ya bayar da tallafin kudi ga masu karamin karfi mutum 6,000 a kanan hukumomin Kebbi ta Tsakiya, sannan ya raba wa manoman shanun huda guda 1,600.

“Ya gina abokan siyasarsa da magoya bayansa sannan har yanzu yana ci gaba da taimaka musu a siyasance, don haka a shirye suke su bi shi zuwa duk inda ya nufa a siyasance.

“Manyan ’yan siyasar APC da dama yaransa ne, kuma idan lokacin zabe ya zo shi za su yi,” in ji kakakin na PDP.

Magoya bayan Aliero sun bayyana cewa ayyukan da ya yi a lokacin da yake gwamna a jihar sun hada ga kafa makarantar koyon aikin jinya, Jami’ar Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kebbi, gina rukunin gidaje na Aliero Quarters  da kuma gina masaukin bakin shugaban kasa da ke Birnin Kebbi.

Sannan ya gina hanyar Jega zuwa Birnin Kebbi, Kebbi zuwa Argungu, da wurin saukan jirgin sama na farko wanda daga baya Gwamnatin Dakingari ta daga darajarsa ya koma babban filin jirgin sama.

Alamun nasarar Bagudu

Sai dai duk da haka, magoya bayan APC ganin damar Bagudu ta lashe zaben ta fi ta Aliero, domin ya fi Aliero farin jini a wurin jama’a saboda kyawawan ayyukan da gwamnatinsa ta yi musu a fadin jihar.

Wani mai goyon bayan Bagudu, Abubakar Bunza, ya ce, “A zaben Sanata na 2011 Aliero ya sha kashi a hannun Bagudu, lokacin da ya tsaya takara a karkashin Jam’iyyar CPC.

“A wannan zabe da ke tafi ma zai kara yin nasara saboda mutanen mazabar shi za su sake zaba tare da Jam’iyayar APC.”

Shari’ar takarar Aliero

A yayin da ake haka, ana ci gaba da shari’a kan takatar Aliero a PDP.

A baya, Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Birnin Kebbi ta soke takarar, amma tuni ya daukaka kara.

Idan Kotun Dukaka Kara da ke zamanta a Sakkwato ta tabbatar da hukuncin, to tsohon Shuganan PDP na Jihar Kebbi, Saidu Haruna, na iya zama dan takarar jam’iyyar.

Idan hakan ta faru kuwa, da alama APC da Bagudu za su kayar da shi cikin sauki a zaben.

Sai dai kuma, har yanzu bangaren Aliero na da kwarin gwiwa cewa kotun daukaka kara za ta tabbatar da  shi a matsayin da takara, kuma zai doke Gwamna Bagudu a zaben da ke tafe.