✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karnukan mai makaranta sun yi kalaci da dalibi

Karnukan sun cinye yaron ne lokacin da iyayensa suka kai shi don yi masa rijista.

Wasu karnuka kimanin su 10 sun cinye wani dalibi mai suna Amokpo Umuanunwa a yankin Nteje da ke Karamar Hukumar Oyi ta Jihar Anambra.

A cewar mazauna yankin, iyayen dalibin sun kai shi makarantar mai suna Global Growth Acdemy ne ranar Litinin da nufin a yi masa rijista.

Sai dai yayin da iyayen ke cuku-cukun yi masa rijistar, sai Amokpo ya fito daga wajen inda su kuma karnukan ba su yi wata-wata ba suka far masa da cizo, sannan suka ja shi zuwa inuwa kafin su cinye shi.

A cewar majiyar tamu, mamallakin makarantar, Chinedu Oka, bai dade da dawowa daga kasar Burtaniya ba kuma yana kiyon karnukan ne a gida daya da inda makarantar take.

Kazalika, binciken Aminiya ya gano cewa ko a al’adance, yankin da lamarin ya faru na Nteje ya haramta kiwon karnuka.

Shi kansa mutumin sai da aka gargadeshi a kan haka amma ya yi kunnen uwar shegu.

Jin labarin hakan ne ya sa matasa masu aikin sa-kai na yankin suka garzaya makarantar, mallakin Chinedu Oka sannan suka harbe dukkan karnukan.

Da yake tsokaci a kan batun, basaraken yankin, Igwe Roland Odegbo ya ce da gangan Chinedu ya bari karnukan suka cinye yaron tun day a san an haramta kiwonsu a yankin.

A cewarsa, la’akari da dokokin yankin, mutumin ya aikata kisan kai ne, inda ya ce tuni ma suka cafke shi tare da damka shi ga hukumomi don ya fuskanci hukunci daidai da laifinsa.

“Matasa sun kashe tare da kone karnuka, muna tare da su,” inji basaraken.

A wani labarin kuma, rahotanni sun ce tuni aka rufe makarantar, yayin da iyaye ke tururuwar cire ’ya’yansu bayan samun labarin.