Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya ta ce kudin da take saya wa karnukanta abinci ya fi wanda ake sayo abincin fursunoni.
Kwanturola Janar na hukumar, Haliru Nababa ya shaida wa Majilisar Dokoki ta Kasa cewa hukumar tana saya wa kowane kare abincin Naira 800 a kullun, kowane fursuna kuma abincin N750 a rana.
Haliru Nababa ne ya bayyana haka ne a yayin da yake kare kasafin 2024 na hukumar a gaban Kwamitin Harkokin Cikin Gida na Majilisar bayan mambobin kwamitin sun tambaye shi yawan karnuka da fursunonin da ke gidajen yarin da abin da ake kashewa wajen ciyar da su.
Shugaban hukumar ya shaida musu cewa faursunoni sama da 81,000 ne ke tsare a gidajen yarin, amma 53,000 suna zaman jiran a yanke musu hukunci ne.
- Kano: Abba ya nada Darakta-Janar kan tallace-tallace a titi
- Harin Mauludin Kaduna ba kuskure ba ne —Sheikh Gumi
Game da abinci kuwa, N750 da ake kashe wa kowanne fursuna a kullun, inda ya ce kudin abincin fursunonin ya yi kadan kwarai, kuma jima da mika wa Ministan Harkokin Cikin Gida bukatar a kara kudin zuwa N3,000.
Ya shaida wa kwamitin cewa hukumar na da karnuka 900 a gidajen yarin, kuma ana kashe wa kowan kare N800 a kan abinci a kullum.
Shugaban Kwaminin Majalisar Dattawa, Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo), ya bayyana mamakinnsa “yadda aka fi ciyar da karnuka a kan fursunonin da yawancinsu masu zaman jiran hukunci ne.”
Oshiomhole ya ce rashin kulawar ce ke sa wasu fursunonin da ake tsarewa kan kananan laifuka suke zama gaggan masu laifi a lokacin da suka gama zaman wakafi.
Ya kara da cewa, “duba da yadda rayuwa ta kara tsada, da wuya idan ma ana ciyar da fursunonin sau uku a rana, amma mun san ba laifinka ba ne,” in ji shugaban kwamitin.