✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karnuka 250 sun mutu a fadansu da birrai

Bayanai sun ce kusan kowane kare a garin an kashe shi.

Birrai a wani birnin Indiya sun kashe karnuka 250, tare da jefo su daga saman manyan gine-gine da bishiyoyi, kamar yadda kafar labarai ta News18 ta ruwaito.

Mazauna yankin Labool, wani gari ne mai kimanin mutum 5,000 da ke da nisan mil 300 a gabas da birnin Mumbai, sun shaida wa News18 cewa, birrai sun fara daukar fansa ne a watan jiya bayan da wasu karnuka suka kashe wani dan biri.

Mazauna yankin sun ce tun daga lokacin ne birrai suka fara farautar karnuka ta yadda da zarar sun hango su sai su ja su zuwa saman dogayen gine-gine ko bishiyoyin suna jefo su kasa don hallaka su.

Birran sukan jefo karnukan ne daga sama, kamar yadda kafar labarai ta News18 ta ruwaito, har sai sun mutu.

Kafar labarai ta Newsweek ta ruwaito cewa, kusan kowane kare a garin an kashe shi.

Newsweek ta ce, an kira jami’ai daga Sashen Kula da Dazuzzuka a yankin don su taimaka wajen kama birran, amma ba su iya kama ko daya ba. Daga nan ne mazauna kauyukan suka yi kokarin kama birran.

News18, ta ce da yawa daga cikin birran sun samu raunuka a kokarin kisan karnukan.

“Birrai a yanzu suna kai hari kan kananan karnuka, suna haifar da ‘firgici’ a yankin Labool,” kamar yadda News 18 ta ruwaito.

Mataimakin Farfesa a Jami’ar SUNY Buffalo, Stephanie Poindedter, wanda bincikensa ya mayar da hankali a kan halayyar halittu wadanda suke da tafin hannu, tafin kafa da kuma fuska mai dauke da idanu da suke fuska kamar dan Adam da birrai, ya ce, “A cikin binciken da aka yi game da irin wadannan halittu da ake killacewa, a cikin wuraren da jama’a ke ziyarta kamar gidajen namun daji, mun gano cewa lokacin da aka kai wa irin halittun hari ta wata hanya, akwai yiwuwar su mai da martani ta hanyar kai hari ga wanda ke da alaka da wanda ya zalunce su, kuma martanin zai fi tsanani fiye da yadda aka kai masu.