Jagoran Jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari dangane da kiran da ya yi ga uwar jam’iyyar kan ta soke karin wa’adin da aka yi wa shugabannin jam’iyyar.
A wata takardar ya sanya wa hannu sannan aka raba ga manema labarai, Tinubu ya bayyana cewa Buhari ya yi abin da ya dace wajen ya fadin gaskiya, kuma kai-tsaye ba tare da nuku-nuku ba.
“Da a ce Shugaba Buhari bai yi magana ba, kila sai a ci gaba da tafiya a karkace a kan tsarin da aka yi na karin wa’adi ga shugabannin jam’iyya a karshen watan Fabrairun da ya gabata, amma sai ya nuna shi mutum ne mai matukar burin ganin ya ja ragamar jam’iyyarsa zuwa ga hanya mikakkiya ba tare da saba kowace doka ba.
“Hakika wannan rana abin farin ciki ce ga dukanin masu kaunar tabbatacciyar dimokuradiyyar da ake fatan dorewarta a kasar nan,” inji shi
Tinubu ya ci gaba da cewa abin da Buhari ya yi, zai kara karfafa jam’iyyar ta hanyar bayar da dama ga mambobinta, ciki har da wadanda ke kan mulkin jam’iyyar a yanzu, wajen ba su damar sake tsayawa takara domin su taimaka wa jam’iyyar kamar yadda suke ganin ya dace.
“Kuma ya kamata jam’iyyar ta hanzarta fara shirye-shiryen gudanar zabubbikan sababbin shugabanni kamar yadda jadawalin zaben shugabannin jam’iyyar ya tsara ba tare da tauye hakkin kowa ba,” inji shi.
A karshe ya ce wannan ba karamar nasara ba ce ga Najeriya da al’ummarta baki daya, don haka ya kamata a yi watsi da tsohon salon siyasar dauki-dora, ta yadda za a rungumi sabon salo mai kara jaddada dimokuradiyya da ba da ’yanci ga kowa.