Gamayyar kungiyoyin farar hula a Jihar Edo ta ce duk wani karin kudin man fetur da na lantarki da ake shirin yi zai kara jefa ’yan Najeriya da dama cikin ha’ula’i.
A yayin da suke tunatar da cewa, ’yan Najeriya dama da cin abinci sau uku a rana ke gagagararsu, Kungiyoyin sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta jingine shirinta na kara kudin mai da na lantarki.
- IPOB: Dokar zaman gida ta samu karbuwa a Anambra
- ’Yan IPOB sun kashe Shugaban Hukumar Shige da Fice a Imo
Da yake magana yayin wani tattaki da aka yi wa lakabai da ‘Ranar yaki da bakin talauci da rashin tsaro a Najeriya’ ranar Lahadi a Benin, Osagie Obayuwana, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kasa domin kare hakkin dan Adam, CDHR, ya ce aikata miyagun laifuka da rashin tsaro a Najeriya rashin aiki ne silar su.
“Akwai nasaba ta kai tsaye tsakanin rashin tsaro da talauci.
“Lallai ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da dukkanin tsare-tsaren da ke cin karo da muradun jama’a.
“Don haka muna amfani da wannan tattaki domin kira ga matasa da manoma da dalibai da masu sana’o’in hannu da sauran jama’a da su fito su ce ya isa haka nan,” inji shi.
Ya shawarci gwamnatoci a dukkanin matakai da su aiki da masu ruwa da tsaki wajen nazartar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki da zimmar kawar da dukkan manufofin da ke gallaza wa talaka.
Sannan ya yi kira ga Gwamnatocin Jihohi da su dakatar da batun shirinsu na rage mafi karancin albashin ma’aikata, maimakon haka su aiki da dokar mafi karancin albashi.