✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin kudin data da kiran waya na nan daram —Gwamnatin Tarayya

Ministar Kudi ta aike da takardar sanarwar fara aiwatar da karin harajin ga Pantami da sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati

Duk da tirjiya da kiraye-kirayen masu ruwa da tsaki da sauran al’umma ke yi, Gwamnatin Tarayya ta ce babu gudu babu ja da baya kan shirinta na kara harajin kashi biyar na kiran waya da data a Najeriya.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce ta riga ta aika takardar sanarwar fara aiwatar da harajin ga Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami da sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati da abin ya shafa.

“Daga yanzu, kamfanonin sadarwa za su karbi harajin kashi biyar cikin 100 na kira da sayen data, kuma za su biya Gwamnatin Tarayya akalla a kowace ranar 21 ga wata,” in ji Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare.

Idan karin ya tabbata dai, ’yan Najeriya za su dinga biyan harajin kashi 12.5 cikin 1oo na kira da sayen data, baya ga kashi 7.5 cikin 100 na harajin kayayyaki da ake biya a yanzu.

Sanarwar da Hadimin Ministar Kudi kan Harkokin Yada Labarai, Tanko Yususa, ya fitar, ta ce harajin zai zamo wani bangare na samun karin kudaden shiga ga gwamnati.

Ya ce ministar, ta riga ta bayyana wa masu ruwa da tsaki matsayar gwamnatin a taronsu da Hukumar Sadarwa ta Kasa ta shirya.

Yayin taron dai ministar, wacce Mataimakin Darakatan Kula da Dokokin Haraji na ma’aikatar, Musa Umar ya wakilta, karin harajin ba yanzu ne Gwamnati ta kirkire shi ba, domin kuwa yana kunshe cikin kundin dokar hukumar na 2020.

A baya dai Pantami ya bayyana rashin amincewar sa da tsarin, har ya yi barzanar yin dukkan mai yiwuwa a dokance don ganin karin bai tabbata ba.

A cewarsa bangaren yana samar da wadataccen kudin shiga ga gwamnati, don haka bai kamata ta yi gaban kanta ba tare da shawartar kwararru ba wajen aiwatar da karin.

To sai dai Ministar Kudi ta dage kan karin, domin a cewarta kasashen Afirka irin su Malawi da Uganda da Tanzaniya na da irin tsarin domin habaka kudaden shigarsu.