✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin albashin ’yan sanda ya dace, sai dai … –Tsav

A makon jiya ne Shugaban Kasa ya kara wa ’yan sanda albashi, wannan ya sa Aminiya ta tuntubi tsohon  Kwamishinan ’Yan Sanda Alhaji ABubakar Tsab…

A makon jiya ne Shugaban Kasa ya kara wa ’yan sanda albashi, wannan ya sa Aminiya ta tuntubi tsohon  Kwamishinan ’Yan Sanda Alhaji ABubakar Tsab kan karin albashin ’inda ya dace sai dai ya kamata su sauya hali su guji cin hanci da maula:

 

Mene ra’ayinka game da karin albashi ga ’yan sanda da Gwamnatin Buhari ta yi?

Karin albashi ga ’yan sanda ya dace matuka, domin a gaskiya albashin ya yi kadan sosai, ganin irin darajar aikin da suke yi ga kasa ba dare ba rana. Ina godiya ga gwamnati da kuma kira ga ’yan sanda su dage domin saka wa karin da alheri irin na mazan jiya. Ban da rashawa da cin hanci da musguna wa talakawa. Abin kunya ne yadda ’yan sanda ke karbar na goro daga masu ababen hawa a wuraren duba ababen hawa da sauransu.

Shin ko karin ya dace a yanzu?

Akwai dalilai da yawa, zabe ya kusa, kuma idon ’yan siyasa ya rufe, don sun matsu su ci zabe kuma za su iya ba da kudi don su cimma manufarsu. Karin albashin ya dace kwarai.

Me ya sa aikin ’yan sanda ya samu koma-baya?

A da lokacin da muke aiki, ana yin aiki ne da gaskiya, ana cewa tsarin “Dry ration” wato ana ba da abincin gwangwani ga masu kwanan daji.

Yaya aka yi a da ’yan sanda suke da kaya da hula da takalma iri daya amma yanzu kowa launin kayansa, dinki da takalmi da suransu daban?

Ya kamata ’yan sanda  su zama masu tattali domin jin dadi a gobe. A lokacinmu, irin kaya da takalmi da dinki duk iri daya ne.

Me ya sa a da idan ’yan sanda za su je aiki, sai a kai su a mota amma a yanzu sai su tafi a kasa dauke da bindiga?

Haka na da ban takaici matuka kwarai. Bai dace ba kuma ya kamata a dauki wanda ya sa hannu ya dauki binidiga ya nufi wurin aiki, kamar yadda ake yi a da. Bai kamata a mayar da aikin kamar na wasa ba. Ya dace a dauki dan sanda daga ofis zuwa inda zai yi aikin wuni ko kwana, sannan a dawo da shi. Bai kamata dan sanda ya tafi a aiki ko ya dawo a motar haya ko a kasa ba, idan ya ci karo da miyagu, suna iya kwace bindigar su yi wa jama’a ta’adda da ita.

Me ya sa hukumar ’yan sanda ba su da asibiti don jinyar wadanda aka jikkata a bakin aiki?

Akwai asibitin ’yan sanda a kowace jiha.

…Ko dai dakunana shan magani?

Eh, dakunan shan magani. Ya dace gwamnati ta gina manyan asibitoci kuma ta inganta su don kula da ’yan sanda.

Wane kira za ka yi ga ’yan sanda da ke zubar da mutumcin aikinsu?

A lokacinmu akwai kima da sanin aiki amma a yanzu abin ya sauya matuka, don a yanzu sai ka ga dan sanda yana rike da jakar madam ko kuma ya daga lema ya rike wa wani wai shi oga. Abin bai dace ba, laifi ne kwarai, ya kamata su rike darajarsu ta aiki.

Me ya sa sanatoci da saurasu ke da ’yan sanda suna bin su har da jiniya amma a yanz?

Ai mutanen Najeriya suna son girma da kece-raini kamar tsiya da son ganin dan sanda ko ’yan sanda suna gadinsu. Wanda abin ya rage darajar aikin dan sanda, har ya mayar da shi abin dariya.

Shin ko karbar kudi daga wadanda suke son shiga aikin ’yan sanda na da alaka da cin hanci?

In matashi ya shiga aiki kyauta zai daraja aikin, idan ya biya rashawa kafin ya shiga aikin, ya zama ya zuba jari ke nan, sai rashawa ta biyo baya. Kuma ya kamata a rika ba ’yan sanda kayan aiki kyauta. A lokacinmu duk wata shida ake ba mu kayan aiki wanda a Turance muke kira ‘Laying of Kits.’ Za ka zube kayan aikinka, sai hafsa ya duba ya ga wanne ne ya kamata a kara maka, kamar yunifom da  sauransu. Amma a yanzu a kasuwa suke sayen kayan aiki da yunifom da takalmi da sauransu kuma bai dace ba. Wannan halin ya sa suke karbar na goro don sayen kayan aiki.

Mece ce mafita?

Ya kamata gwamnati ta nuna daya daga masakun kasar nan da za ta rika saka kayan aikin ’yan sanda, ba ka ga ’yan sanda suna sa kaya amma launi daban-daban ba.