A karon farko cikin shekara 106 da kafa kungiyarsu, ma’aikatan jinya a duk fadin Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta tsunduma yajin aiki saboda kin yi musu karin albashi.
Rahotanni sun ce kungiyar ta ce zaben jin ra’ayin mambobinta da ta gudanar ya nuna cewa akasarinsu na goyon bayan a shiga yajin aikin a kwanan nan.
- Dorinar ruwa: Dabbar da ke iya rike numfashi tsawon minti 5 a cikin ruwa
- Kamfanin ‘Facebook’ na shirin sallamar ma’aikata 11,000
Ministan Lafiya na Birtaniya, Steve Barclay, ya bayyana yunkurin ma’aikatan a matsayin abin takaici.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta ce tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyakin da ake fama da su a kasar sun sa mambobinta sun koma rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya.
“Wannan lokaci ne mai cike da kalubale a tarihin gwagwarmayarmu, kuma fafutukar da muke yi za ta ci gaba yayin yajin aikin da ma bayan kammala shi, har sai an inganta mana sana’a,” inji Sakatariyar kungiyar, Pat Cullen.
“Wannan shi ne mataki na karshen da za mu iya dauka. Mambobinmu na cewa tura fa ta kai bango,” inji ta.
Ana sa ran yajin aikin zai fara kafin karshen wannan shekarar, kuma za a sanar da ranar fara shi nan ba da jimawa ba.
Ma’aikatan dai na neman a kara musu albashi ne da kaso biyar cikin 100 saboda tashin gwauron zabon da farashin kayayyaki ya yi a kasar a ’yan watannin nan.
Ma’aikata a bangarorin ayyuka daban-daban na kasar ne suka shiga yajin aiki a kasar daga farkon bazarar bana ya zuwa yanzu. (AFP)