Gwamnatin Tarayya ta lashe amanta kan batun karin albashin ma’aikata a shekarar 2023 mai kamawa.
Gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da niyyar kara wa ma’aikatanta albashi kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke rade-radi.
- An tura dan sandan da ya kashe lauya gidan yari
- An daure matashi shekara 14 kan yi wa karamar yarinya fyade
Ta bayyana cewa sabanin karin albashi da ake rade-radi, “wasu alawus-alawus na musamman ne kawai” take shirin kara wa ma’aikata.
Ministan Kwadago, Chris Ngige, ne ya sanar da haka ta wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatarsa, Olajide Oshundun ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce tuni aka mika wa Kwamitin Albashi na Fadar Shugaban Kasa karin alawus din wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati ta hannun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
A cewarsa, ana fata karin zai rage wa ma’aikata radadin hauhawar farashin kayayyakin masarufi da na ruwa da wutar lantarki da sauransu.
Ngige ya bayyana cewa karin ba zai shafi gundarin albashi, saboda yin hakan yana bukatar tattaunawa da kungiyoyin kwadago a matsayin wakilan ma’aikata.