✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Karin albashi ga ’yan sanda ba zai yi tasiri ba – Rafsanjani

Auwal Musa Rafsanjani shi ne ne Babban Daraktan Kungiyar Cibil Society Legislatibe Adbocacy Center (CISLAC), sannan shi ne Shugaban Kungiyar Transparency International, kuma shugaban kwamitin…

Auwal Musa Rafsanjani shi ne ne Babban Daraktan Kungiyar Cibil Society Legislatibe Adbocacy Center (CISLAC), sannan shi ne Shugaban Kungiyar Transparency International, kuma shugaban kwamitin amintattu na Amnesty International a Najeriya. Ya bayyana wa Aminiya cewa karin albashin da aka yi wa ’yan sanda ba zai yi tasiri wajen inganta tsaro da kawar da cin hanci da rashawa:

 

Wane tasiri kake jin karin albashin da aka yi wa ’yan sandan Najeriya zai yi?

A gaskiya wannan karin albashin ba wani tasiri zai yi ba. Babban abin da Shugaban Kasa ya kamata ya fara la’akari da shi, shi ne gyara tsarin da ake bi wajen daukar ’yan sandan aiki tun a nan ake fara almundahanar. A san wadanne irin mutane ne ake dauka aikin. A gyara yanayin ofisoshinsu ciki har da inda ake tsare jama’a da kuma barikokinsu, inda iyalansu suke. Ya duba yadda ake karin girma da sakayya ga wadanda suka yi abin kirki ko kuma ladabtarwa ga wadanda suka aikata laifi. Ya samar da isassashen kudin gudanar da ofisoshinsu, sabanin tatsar jama’a da suke yi don sama wa kansu mafita, ciki har da zuba wa motocinsu mai da makamantansu. Sai kuma kayan aiki da ba da horo a kai-a kai ta yadda zai dace da zamani. Wadannan su ne tarin matsalolin da suke fama da su, wadanda a yanzu aka dan waiwayi guda daya. Ga matsalar zargin amsar kudi kafin a tura dan sanda zuwa wani waje da zai iya samun kudin kirki.

Amma don ka kara wa dan sanda albashi na Naira dubu 30 wanda bai kai Dala 100 ba, wane tasiri hakan kadai zai iya yi saboda Allah a cikin tarin wadannan matsalolin da suke fama da su? Suna bukatar tsarin inshora saboda a yanzu da dama daga cikinsu idan mutum ya rasa ransa a wajen aiki shi ke nan babu wanda zai kula da iyalansa da ya bari. Suna bukatar a karfafa musu gwiwa fiye da karin Naira dubu 30, wanda ni a ganina tamkar abin nan ne da Bature ke cewa ‘window dressing’ kawai amma ba hakikanin gyaran da ake bukata ba.

Kun samu tabbacin cewa wannan shi ne kari da aka yi?

Eh, to wannan shi ne irin abin da muka samu labari a kai daga kafofin watsa labarai duk da cewa ba mu da tabbacin hakan. Karin ya rabu mataki-mataki, amma dai wannan shi ne abin da muka ji an yi wa kurata. Sai dai kana iya bincike a kai kada ya kasance na ba ka alkaluma marasa inganci.

Ire-iren wadannan abubuwa da suka zo daf da lokacin zabe wadansu na danganta lamarin da siyasa, me za ka ce a kai?

A gaskiya ba za ka iya karyata masu irin wannan ra’ayi ba, saboda suna da hujjar da suka bayar, tana da karfi. Shin me ya sa gwamnati ta san da wannan lamari tuntuni amma ba ta dauki mataki a kai ba, sai a yanzu da take da ragowar kasa da shekara daya cikin wa’adinta na shekara 4, kuma har ma an fara harkar zabe? Ka ga idan ka dubi lamarin ta wannan fuska da kuma yadda aka nuno ’yan sanda suna tsalle suna sai Baba, kana iya cewa biri ya yi kama da mutum.