A ranar Lahadin da ta gabata Ce Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta janye yajin aiki na gargadi da ta fara a ranar alhamis 27 ga watan Satumba, inda take bukatar a kara wa ma’aikata albashi daga Naira dubu 18 zuwa Naira dubu 50 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
Kungiyar Kwadagon ta ce ya zama dole a kara wa ma’aikata albashi sakamakon tsananin tsadar da rayuwa take da shi a halin yanzu, wanda ya sanya ma’aikata suke fuskantar matsananciyar wahala.
An dade da fara gwagwarmayar bukatar karin albashi, inda tarihi ya nuna cewa an fara gwawarmayar a kasar nan ce a 1945. Amma lamarin ya fito fili sosai ne a 1981 lokacin da Kungiyar Kwadago ta bukaci a kara albashi ya zama Naira 300 ne karancin abin da za a biya ma’aikaci a kasar nan, an yi wannan ne a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Kwadago na wancan lokaci Hassan Summonu, inda gwamnatin Shehu Shagari na lokacin ta amince a biya Naira 125 a matsayin mafi karancin albashi.
Bayan wannan kuma an sake wata tattaunawar domin karin albashin a tsakanin 1989/1990 a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Kwadago na lokacin Pascal Bafayau, wanda Mataimakinsa Adams Oshiomhole (Shugaban Jam’iyyar APC a yanzu) ya jagorancin zaman, inda aka amince za a rika biyan Naira 250 a matsayin mafi karancin albashi.
Sai kuma aka sake wani zaman a 1998/1999 a zamanin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar inda aka amince za a rika biyan Naira dubu 3 da 500. Kodayake da farko gwamnatin Abdulsalami ta yi karin albashin ne zuwa Naira dubu biyar a matsayin albashi mafi karanci, har an fara biya, ma’aikata suna ta murna, sai gwamnati ta rage zuwa Naira dubu 3, bayan an yi tunzuri ne aka daidaita a kan Naira dubu 3 da 500. Hujjar gwamnatin Abdulsalam na rage albashin shi ne saboda la’akari da ta yi cewa farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya a lokaci yana ta fadowa kasa, har sai da ya fado zuwa Dala 9, saboda haka gwamnati ta rage albashin domin kada ta bar wa gwamnatin farar hula da ake shirin mika mata mulki a 1999 da matsala. Bayan Janar Abdulsalami ya bar mulki ya ce ya yi nadamar rage albashin da ya yi, domin daga baya farashin danyen mai ya yi ta tashi har sai da ya haura Dala 100.
Haka an yi wani zaman a lokacin da Adams Oshiomhole yake Shugaban NLC a tsakanin shekarar 2000/ 2001 inda aka amince a biya Naira dubu 5 da 500 ga ma’aikatan jihohi da Naira dubu 7 da 500 ga ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da kuma na jihohin da ake samar da mai a matsayin albashi mafi karanci, tare da yarjejeniyar cewa idan shekara ta zagayo (2002) za a kara kashi 15, bayan shekara guda kuma (2003) za a kara kashi 25, sai dai kuma gwamnati ta kasa cika alkawarin karin kashi 25 din, sai dai karin kashi 15 ta yi a shekarar 2007, kuma ta kara wa masu rike da mukaman siyasa kashi 800 na albashinsu.
Tun a shekarar 2008 ne Kungiyar Kwadago ta fara fito da bukatar a kara albashi zuwa Naira dubu 52 a matsayin mafi karanci, daga nan aka ci gaba da tattaunawa har zuwa wannan lokaci da ta yi yajin aiki na gargadi game da bukatar tata.
Sai dai kuma a yayin da Kungiyar Kwadago ke ganin karin albashi ne zai fitar da ma’aikaci daga halin kuncin da ya shiga, masana na ganin karin albashi babu abin da zai haifar wa ma’aikaci sai matsala. Domin idan aka lura tun daga 1975 da aka yi karin albashi na Udoji farashin kayayyaki suka rika mugun tashi, haka nan farashin kaya ke tashi duk lokacin da aka kara albashi, wanda hakan ya sanya ma’aikaci ba ya more karin da aka yi.
Maimakon a kara albashi kamata ya yi Kungiyar Kwadago ta dage wajen ganin an samar da muhimman abubuwan more rayuwa ga daukacin a’umma, domin idan aka samar da hanyoyi masu kyau a yankunan karkara manoma za su samu saukin fitar da kayan nomansu zuwa kasuwa, kuma za su samu kayan noma da sauki, hakan zai sa farashin kayan abinci ya sauko, domin za a yi noma da yawa.
Haka kuma idan aka saukaka harkar ilimi albashi zai yi auki, haka abin yake ga harkar lafiya, idan gwamnati ta samar da asibitoci da ma’aikata da kayan aiki da isassun magunguna a farashi mai sauki, albashi zai yi auki. Idan gwamnati ta samar da gidaje a farashi mai sauki, ma’aikata suna biya a hankali albashi zai yi tasiri, idan gwamnati ta taimaka wa ma’aikaci ya mallaki abin hawa albashinsa zai amfane shi. Ko kuma gwamnati ta samar da inganttaciyar hanyar sufuri ta hanyar inganta harkar jiragen kasa da saukaka harkar sufurin jiragen sama yadda mai karamin karfi zai amfana.
Shi ya sanya a shekarun baya ake cewa albashi yana da auki ga ma’aikaci, domin a lokacin an dauke masa jidalin makarantar ’ya’yansa da dawainiyar magani da samar da tallafi a sauran al’amuran rayuwa.
Amma yanzu an sakar wa talaka komai, shi ne zai biya kudin makaranta da kudin littattafai da kayan makaranta da komai da komai da ake bukata a makaranta, haka idan rashin lafiya ta taso shi ne zai ji da kansa, babu wani taimako da zai samu, ta yaya albashi zai yi auki a irin wannan halin komai yawan albashin?
Saboda haka maimakon Kungiyar Kwadago ta rika nacewa sai gwamnati ta kara albashi, kamata ya yi ta rika dagewa wajen tilasta wa gwamnati tana samar da muhimman abubuwan da za su taimaka wa jama’a su ji saukin rayuwa, ta haka ne kawai za a rage wa ma’aikaci matsalar rayuwa amma ba ta hanyar karin albashi ba.
Shi kansa Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshiomhole da ya zama Gwamna a jiharsa ta Edo ya yi rikici da ma’aikatan jihar a kan karin albashi saboda ya fahimci cewa kara wa ma’aikata albashi a yi watsi da sauran muhimman ayyukan inganta rayuwa ba zai yi wa jiharsa kyau ba. Kuma ga shi a halin yanzu shi ne Shugaban Jam’iyyar Gwamnatin da ke mulki, amma da yake ya fahimci cewa karin albashin ba shi ne mafita ba, ai ya yi shiru ne bai taimaka wa Kungiyar Kwadagon ba, duk da cewa ita ce ta fito da shi duniya ta san shi har ya kai matsayin da yake a yau.
Ma’aikata ’yan kalilan ne a kan sauran jama’ar kasa, idan aka ce za a rika kashe kudin kasa wurin kara albashi, kowa da kowa har da su ma’aikatan za su wahala. Saboda haka da karin albashi gara karin ayyukan inganta rayuwar al’umma baki daya.