An bayyana cewa yanzu jam’iyyar PDP tana samun karfin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan saboda samun shugaba jarumi kuma wanda yake da kwarewa a sha’anin jagoranci.
Wannan tsokaci ya fito ne daga jigo a jam’iyyar, Alhaji Musa Saye a zantawar su da wakilin mu a karshen mako, inda ya nunar da cewa ko shakka babu Sanata Ahmed Makarfi ya san makamar aiki sannan dan siyasa ne wanda yake da kaifin tunani na tafiyar da jam’iyya tun lokaci mai tsawo.
Ya ce yanzu karfin jam’iyyar PDP ta fara dawowa a kowane lungu da sako na wannan kasa tamu, sannan su kan su ‘yan jam’iyyar suna matukar maraba fa hukuncin da kotun kolin kasar nan ta yanke na tabbatar da Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar wanda hakan abin a yaba ne.
Alhaji Musa Saye ya kuma sanar da cewa jam’iyyar APC ta gaza wajen samar da ababen more rayuwa ga al’ummar kasa don haka yana da kyau a sami sauyi ta yadda kowane dan kasa zai sami jin dadin zamantakewa da shugabanci mai riba, tare da yin fatan alheri ga Sanata Makarfi da sauran shugabannin jam’iyyar ta PDP.
Dangane da abubuwan da suka faru a baya kuwa, Alhaji Musa Saye ya bukaci dukkanin ‘ya’yan PDP na asali da suka fice da su dawo cikin ta ayi tafiya domin farfado da martabar wannan kasa akan sabuwar tafiya, sannan ya yi godiya ga dukkanin wadada suke da hannu wajen tabbatar da kawo karshen dambarwar da jam’iyyar ta shiga.
Da yake tsokaci kan abin da ya faru a karamar hukumar Bichi kan shugabanci kuwa, Alhaji Musa Saye ya ce anyi masa rashin adalci domin kuwa shine ya kamata ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar ta PDP a karamar hukumar sabanin yadda wasu suka canza al’amura wadda bai yi wa dukkanin magoya bayan jam’iyyar dadi ba.
Sai dai ya sanar da cewa yana nan daram cikin jam’iyyarsa kuma zai ci gaba da yi mata aiki amma yana da kyau a duba rashin adalcin da aka yi na shugabanci a karamar hukumar Bichi da kuma karamar hukumar Rogo domin a sami masalaha musamman ganin irin gudummawar da suke baiwa jam’iyya ba tare da nuna gajiyawa ba.