Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dokokin tarayya ta lamince masa ya karbo bashin Dala biliyan biyar da digo biyar daga kasashen waje don ya tallafa wa manyan ayyukan da ke kasafin kudin shekarar 2017 tare da biyan basussukan cikin gida.
A wasikar da ya rubuta wa ’yan majalisar a ranar 4 ga watan Oktoba wacce Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da kuma Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara suka karanta jiya.
Shugabannin Majalisar sun karanta wasikar ne mako guda bayan da Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta yi zargin cewa majalisar dokokin tana jan kafa wajen amincewa da karbo bashin.