Fitaccen dan kasuwa a Najeriya, Alhaji Sani Yunusa Sarina (Sani Brothers) ya ce zalunci ne shirin Gwamnatin Tarayya na karbo bashin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya domin rage radadin janye tallafin man fetur da za ta yi.
A kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya nemi sahalewar majalisar dokoki ta kasa don karbo bashin domin raba wa talakawa da nufin rage musu radadin cire tallafin mai da gwamnatinsa ta so yi.
Zalunci ne kawai —Sani Brothers
Amma a yayin hirarsa da ’yan jarida a Kano, Alhaji Sani Brothers, wanda tsohon Shugaban Kungiyar Masu sufuri ta Kasan ne ya bukaci gwamnati da sake tunani, domin a babu amfanin da karbo bashin zai yi, sai da ma ya cutar da jama’ar Najeriya.
A cewarsa, “Ban taba ganin inda aka karbo bashi aka yi kyauta ba. Ta yaya za a karbi bashi a ba wasu tsiraru wanda ba su fi kaso 10 cikin 100 ba, sannan a bar nauyin biyan bashin a kan alummar kasa gaba daya, wadanda ba su ci ba, ba su sha ba?”
A cewar Alhaji Sani Brothers, za a iya cire tallafin mai ba tare da ciyo bashi da kuma rabawa ga wasu tsiraru ba.
“Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya cire tallafin mai kuma bai karbo bashin ko kwabo ba har daga baya aka dawo da tallafin.
“To me ya sa ita wannan gwamnatin za ta fito da wannan magana, ko ita nata shirin daban ne?”
Ya ci gaba da cewa karbo bashin ba zai amfanar da alumma ba, illa cutuwa gare su.
“Ya kamata shugabanni su daina kawo abubuwan da za su cutar da talakawansu. Wannan bashi cutarwa ce ga talakawan domin kasarsu ce za ta biya.
“Kuma ba su ne za su amfana da kudin ba, wasu ne wadanda ba talakawan ba za su amfana da bashin.”
Tsohon bashi ba ne —Bankin Duniya
Bankin Duniya, ta bakin daraktansa a Najeriya, Shubham Chaudhuri, ya bayyana cewa bashin ba sabo ba ne, kuma tun watan Dismanban shekarar 2021 mahukuntan bankin suka amince da bakatar Najeriya ta karbar rancen.
Shubham Chaudhuri ya kara da cewa, karba ko kin karbar kudin hurumin ne na gwamnati mai jiran gado, kuma majalisa na da ikon amincewa ko watsi da bukatar sa hannu.
A cewarsa, samun izinin majalisar da Buhari ke yi ne zai saukaka wa sabuwar gwamnati amfani da kudaden idan tana bukata, domin bayar da tallafin janye tallafin man fetur.
Chaudhuri, ya ce “idan sabuwar gwamnatin za ta janye tallafin mai, za ta iya karbar kudaden babu bata lokaci, maimakon sai ta sake komawa neman sahalewar majalisa.
“Wannan gwamnatin saukin karbar kudaden kawai take nema wa wadda za ta gaje ta, idan har tana da ra’ayin janye tallafin man.
“Idan ba haka ba, sai an samu karin akalla wata shida ana kai-komo a kai kafin Kwamitin Daraktocin Bankin Duniya su amince.
“Haka kuma, idan kuma sabuwar gwamnati ba ta bukatar rancen, za ta iya soke bukatar, sannan ko da majalisa ta amince a karbo, ba dole ne gwamnatin ta karbo kudaden ba.”