✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karbar katin zabe: Gwamnan Kwara ya bai wa ma’aikatansa hutun kwana guda

Gwamnatin jihar ta ba da hutun ne don bai wa ma'aikatanta zarafin su je su karbi katin zabensu.

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, ya bai wa ma’aikatan jihar hutun kwana daya domin ba su damar zuwa karbar Katin Zabe.

Shugabar Ma’aikan Jihar, Susan Oluwole ce ta bayyana hakan ranar Talata a Ilorin, babban birnin Jihar.

Susan ta ce an ba da hutun ne musamman don ma’aikata su samu zarafin zuwa karbar katin zabensu.

Ya ce, “Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya amince da ranar Laraba, 25 ga Janairu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati a Jihar domin bai wa ma’aikatan damar shiga zabe mai zuwa yadda ya kamata.

“Dukkan wadanda ba su karbi Katin Zabe ba su tabbatar da sun yi hakan kafin karewar wa’adin da aka tsayar don kammala aikin raba katin zabe,” in ji Oluwole.

(NAN)