Rayuwa ba ta taba ci gaba ba in babu ilimi. Kowace al’umma na kokarin ta ga ta ci gaba wajen samar da ingantaccen ilimi.
Karatun ’ya’ya mata na da matukar amfani, koda a ce sun yi aure hakan ba zai kawo musu wata matsala ba, don sun ci gaba, sai dai ya kara karfafa musu gwiwa wajen samar da ingantacciyar al’umma.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Siyasa Ke Raba Kan ’Yan Najeriya, Su Kuma Kansu A Hade
- Dalilin da ya sa ake tsoron aurenmu —Mata ’Yan Boko
Karatu ba ya hana aure kamar yadda aure ba ya hana karatu. Duk macen da ta yi karatu, rayuwarta na bambanta da ta sauran mutane, ta yadda za ta yi mu’amala da al’umma, tare da gyaran dabi’unta, tarbiyyarta da ta ’ya’yanta da sauransu.
Abin bakin ciki shi ne, akwai wadanda suke daukar karatun ’ya mace mara amfani, musamman matan aure da suke gidajensu.
Wasu mazan sukan yi mummunar fahimta ta yadda za ka ga namiji na cewa, duk macen da ta yi karatu musamman na boko ta fara aiki tana daukar albashi takan fi karfin mijinta.
Sai ka ga maza da yawa suna hana matansu karatu, wani idan matar ta matsa sai ya kai ga karewar aure.
Baya ga haka, kamar yadda dutse daya ba ya kara shi kadai, su ma mata suna da tasu matsalar.
Za ka ga mace a gaban iyayenta ko a gidan mijinta a natse tana aiwatar da komai yadda ya kamata, tare da bayyana biyayyarta ga mijinta da iyayenta, amma da zarar ta bar gida ta tafi makaranta, daga nan kuma Shaidan zai fara zuga ta saboda rauninta.
Matar aure ce, amma sai ka gan ta a tsakiyar maza ana tadi da ita tana daga murya bayan ta san hakan ba daidai ba ne.
Wasu ’yan matan ba za ka so ka kara ganinsu ba, idan ka kalli yanayin da suke ciki a makaranta, rayuwarsu gaba daya canzawa take yi idan sun je makaranta. Suna daukar wata rayuwa wacce ba ta dace da su ba su daora wa kansu.
A maimakon su yi abin da ya kai su, sai ka ga sun biye wa kawaye da wasu malamai da abokai, wanda hakan ba shi ba ne hanya mafi dacewa a gare su. Ya kamata mata mu kiyaye mutumcinmu.
Rayuwar ’ya mace gajera ce ko mun ki ko mun so, wannan ita ce gaskiya.
Duk lokacin da dama ta samu to kada ki yi wasa da damarki ki yi shashanci da abin da bai dace ba. Duk lokacin da kika samu kanki a matsayin daliba wacce take karatu to ki zamo mai kiyayewa.
Ki zamo mai kamun kai da natsuwa da kuma kiyaye mutuncinki. A karshe, ya kamata mai karatu ya san cewa, karatun ’ya mace haske ne ga al’umma, domin su ne suke tare da yara koyaushe.
Tabbas masana sun yi gaskiya da suka ce, “Mother is the first teacher.”
Idan mace ta yi karatu za ta iya haifar da al’umma ta kwarai. Kamar yadda tarbiyya take farawa daga gida, ilimi shi ne hasken rayuwa.
Daga karshe ’yan uwa ku kyautata niyyarku a kan ’ya’yanku. Ku ba su ilimi mai inganci domin ilimi shi ne ginshikin rayuwa!
Daga Fatima Sulaiman Hussaini, daliba a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Za a iya tuntubarta ta [email protected].