Gwamnatin jihar Kano ta haramta tsarin karatun almajiranci wanda ake alakantawa da bara a fadin jihar.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya haramta karatun almajiranci yana mai cewa za a dauki dukkan almajiran jihar da aka dawo da su a makarantun boko.
Ya ce gwamnatinsa ta shirya daukar almajiran a makarantun firamare domin ba su ilimi na wajibi kuma kyauta a matakin farko.
Ganduje ya ce a dokar jihar Kano “Jazaman ne kowane har da almajirai a jihar Kano ya rika halartar makaranta.”
- Almajiri dan Nijar na cikin wadanda jihar Kano ta mayar Kebbi
- El-Rufa’i zai daure iyayen yaran da ke bara
- An kama mutum 5 na yunkurin kashe almajiri domin tsafi
An mika almajirai ga iyayensu.
Kwamishinan Kanan Hukumomi Murtala Sule Garo ya ce jihar ta mayar da yara 1,172 da ke bara a jihar Kano zuwa jihohinsu na asali. Ita kuma an dawo mata da fiye da almajiranta 1,000.
Shugaban na Kwamitin Kwashe Almajirai a jihar ya kara da cewa sun mayar da 723 da ke bara a cikin jihar zuwa hannun iyayensu.
Almajirai 28 sun kamu da coronavirus.
A jawabinsa kan halin cutar COVID-19 a jihar, Ganduje ya ce 28 daga cikin almajiran da aka dawo da su jihar na dauke da cutar.
Ya ce tuni aka killace almajiran kuma suna samun kulawar da ta dace.