✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Karancin tarbiyya daga iyaye ne ke rura wutar matsalar tsaro’

Mohammad Gabdo ya ta'allaka yawan aikata laifuka da ma matsalar tsaro kan karancin tarbiyya daga iyaye to

Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) a jihar Adamawa, Malam Mohammad Gabdo ya ta’allaka yawan aikata laifuka da ma matsalar tsaro kan karancin tarbiyya daga iyaye da kuma rashin nagartaccen shugabanci.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawar sa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Yola, jihar Adamawa ranar Asabar.

Mohammed ya zargi iyaye da rashin daukar nauyin tarbiyyar ‘ya’yansu yadda ya kamata da cewa shine ummul-aba’isun tabarbarewar harkokin tsaron Najeriya.

Ya ce,  “Iyaye sune tushen duk wani kalubalen tsaro kama daga ta’ammali da miyagun kwayoyi, garkuwa da mutane, safarar jama’a, zinace-zinace da dai sauransu saboda ba su dauki nauyin da ya rataya a wuyan su yadda ya kamata ba.

“Wasu na alakanta matsalar da siyasa da rashin shugabanci na gari, amma idan ka yi duba na tsanaki za aka gane cewa masu aikata duk wani aikin masha’a duk ‘ya’yanmu ne.

“Dole mu sa ido a kan su, ta hanyar kula da duk wani motsin su da basu shawara ta gari.

“Idan muka gaza yin hakan, to tabbas za su fada ayyukan masha’a,” inji shi.

Daga nan sai daraktan ya yi kira ga iyaye kan su kara jajircewa wajen tarbiyyar ‘ya’yansu domin ci gaban kasa, yana mai cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya ba.