Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar ta baci kan matsalar karancin ruwan famfo a jihar.
Gwamnan ya bayar da wa’adin mako guda ga Hukumar Ruwa ta Jihar Kano da su mika bukatunsu tare da kawo karshen matsalar karancin ruwa da ake fama da ita a jihar.
- Abba Gida-Gida ya nada shugabannin Hukumar Alhazai
- Abubuwan da muka amfana da su a mulkin Buhari — ’Yan Najeriya
Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci matatar kula da ruwa ta Challawa da yammacin ranar Talata.
Ya ce wannan na daga cikin matakan da gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen dakile matsalar karancin ruwa a fadin jihar.
A yayin ziyarar, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yanayin da ya samu kayan aiki a matatar da ruwan, inda ya ce nan ba da jimawa ba batun karancin ruwan zai zama tarihi a Jihar Kano.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta cika alkawuran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe, don haka ya bukaci mazauna Kano da su ba shi hadin kai.
Da yake karin haske ga gwamnan, Darakta a matatar ruwa ta Challawa, Sakabu Lawal, ya bayyana cewa, injinan bututun ruwa guda biyu ne kawai a cikin shida suke aiki.
Aminiya ta ruwaito cewa a baya-bayan nan mazauna jihar sun koka kan yadda matsalar karancin ruwa ke neman zama barazana a gare su.
Idan za a iya tunawa, batun karancin ruwan sha a jihar bai tsaya iya cikin kwaryar Kano ba, matasalar ta fantsama har zuwa karkara.