✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da muka amfana da su a mulkin Buhari — ’Yan Najeriya

’Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan me suka amfana da shi a mulkin Buhari.

Bayan da Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya mika mulkin kasar ga sabon shugabanta Bola Tinubu a ranar Litinin, al’umma na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da halin ci gaba ko akasinsa da ya bar kasar a ciki tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulki.

Dangane da haka ne Aminiya ta zaga don jin ta bakin ’yan Najeriyar kan abubuwan da suka amfana da su a mulkin Buhari.