Cibiyar Rajistar Malamai ta Kasa wacce atakaice ake kira (TRCN) ta ce karancin malaman da ake fama da shi a kasar nan ya yi kamari.
Cibiyar ta ce lamarin ya kai kimanin malamai miliyan 1 da digo takwas ne suka sami lasisin koyarwa a kasa baki daya.
Shugaban Cibiyar, Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye ne ya yi furucin a ganawar da ya yi da manema labarai, a jiya, a Abuja.
Ya bayyana cewa duk da karuwar yawan dalibai da kuma yawan makarantu, malamai miliyan daya da digo takwas ne kawai suka sami lasisin koyarwa wanda hakan ke nuna karancin malami a kasar ya kai mutuka.
Ya bayyana cewa har zuwa watan Agustan shekarar 2016 malamai miliyan daya da digo biyar ne kawai cibiyar ta yi wa rajista.
Ya ce Cibiyar ta ba yar da karin lasisi ga malamai dubu 130 da 645 tsakanin 2 ga watan Agusta shekarar 2016 da ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2017.
Ya kara da cewa cibiyar za ta fitar da sunayen malaman da ke koyar da kowane darasi a kowace jiha sannan kuma za ta sallami dukkanin malamain da ba su da rajista daga makarantu daga shekara mai zuwa.