✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karancin Mai: DSS Ta Ba NNPC Da IPMAN Wa’adin Sa’a 48

DSS ta yi barazanar farautar duk masu hannu wajen haifar da karancin man

Hukumar tsaro ta DSS, ta bai wa Kamfanin Fetur na Najeriya (NNPC) da Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) wa’adin sa’o’i 48 su kawo karshen matsalar karancin mai da ake fuskanta a kasa.

DSS ta yi barazanar za ta fara farautar duka wadanda ke da hannu wajen haifar da karancin man muddin aka ci gaba da ganin dogayen layin ababen hawa a gidajen mai bayan cikar wa’adin da ta sanya.

Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, jim kadan bayan da Darakta-Janar na DSS, Yusuf Bichi, ya yi wata ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin mai.

Ya ce masu ruwa da tsakin sun amince su shawo kan matsalar karancin mai da ake fuskanta a fadin kasar.

Ya kara da cewa, tuni an fargar da ofisoshin DSS a jihohi kuma za su fara aiki domin kamo wadanda suka ki bin doka.