Karancin man fetur ya kunno kai a cikin Birnin Tarayya, Abuja, da kewaye a ranar Talata.
Yanayin ya sa gidajen mai da dama kullewa tare da haifar tsadar man fetur a garin.
- #EndSARS: Rarara ya saka kyautar Motoci da kudade a gasar Mawaka kan zaman lafiya
- Ministocin Buhari 2 sun bukaci sarkin Kano ya tsawatarwa masu zanga-zanga
Kakakin Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Kennie Obateru, ya danganta karancin man da zanga-zangar #EndSARS, amma ya ba da tabbacin cewa mai zai wadatu a ranar.
Obateru ya ce ’yan kasuwa da dama sun fara samun lodin man da zai kawar da karancinsa.
A zagayen gari da Aminiya ta yi, ta gano matsaloli a yadda ake sayar da man a wasu gidajen mai a Abuja.
A gidan man NNPC na Area 10, kofar daya aka bude da motoci na gwamutsuwa wajen shiga, wanda hakan ya haddasa cunkoso.
A gidan man Total ma ba ta sauya zani ba, sai kuma ’yan bunburutu da suka cika wurin suna sayar wa masu motoci da tsada.
Wakilinmu ya ga ’yan bunburutun na sayar da galan mai cin Lita 4 a kan N1,000 zuwa N1,200
A gidan Man A.A Rano da ke Jabi kuma, wakilinmu ya ga cinciridon ababen hawa na kokarin shan mai.
Lamarin bai canja ba a gidan man NIPCO da ke Jabi inda shi ma aka cika shi makil.
Zanga-zangar #EndSARS dai an fara ta ne cikin lumana amma daga baya ta rikide zuwa rikici bayan zauna-gari-banza sun shiga ciki suna kone-kone da satar dukiyoyin gwamnati da na al’umma.
Daga baya bata-gari sun rika fasa rumbunan gwamnati da aka ajiye kayan tallafin COVID-19 suna kwashewa.
Kungiyar Manya ’Yan Dillalan Man Fetur ta Najeriya (MOMAN), ta ce ba za ta yi magana kan lamarin ba.