✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karamar Hukumar Kafin Hausa ta bullo da dabarun magance rikicin makiyaya da manoma

karamar Hukumar Kafin Hausa ta kudiri aniyar dakile rikicin Fulani makiyaya da manoma a yankinta. Shugaban karamar hukumar Alhaji Garba Bao Muhammed Tambale ne ya…

karamar Hukumar Kafin Hausa ta kudiri aniyar dakile rikicin Fulani makiyaya da manoma a yankinta. Shugaban karamar hukumar Alhaji Garba Bao Muhammed Tambale ne ya shaida wa Aminiya haka a makon jiya. Shugaban ya ce karamar hukumar ta kafa wani kwamiti mai karfi da ya tuntubi karamar Hukumar Bunai da ke Jamhuriyar Nijar domin hana Fulani makiyaya shigowa suna haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin. Alhaji Bako Tambale ya ce sun gindaya sharudda a tsakaninsu da Bunai cewar kafin a bar Fulani makiyaya daga yankin su shigo Najeriya dole sai sun cika sharuddan da hukumar Kafin Hausa ta gindaya da suka hada da cewa dole su shigo bisa jagorancin wani shugaba kuma sai manoma sun kwashe kayan gonarsu kuma ba a yarda su sare wata bishiya ba sai da izinin hukuma kuma kada su taba harawa ko kara sai sun samu izinin mai gona ko sun saya a wajensa. Sauran sharuddan sun hada da cewa su ma masu gonaki dole ne su gaggauta kwashe amfanin gonarsu musamman abinci daga nan zuwa karshen watan Disamba, lokacin da hukuma ta ba Fulani Udawa damar shigowa yankin. Ya ce kuma ba a yarda makiyayan su saki rakuma a kan tituna ko daji suna kiwo ba tare da mai kula da su ba domin magance aukuwar hadduran ababen hawa. Kuma ya ce an sake wani kwamiti da zai sake zuwa Bunai da ke Nijar a karkashin shugabancin Hakimin Kafin Hausa Alhaji dan Amar domin inganta dangantaka tsakanin hukumomin biyu.