A wannan mako ne Majalisar Dattawa ta kammala tantance sunayen wadanda Shugaba Buhari ya mika mata domin nada su a matsayin ministocinsa.
Watanni biyu ke nan da rantsar da Shugaba Buhari domin ci gaba da mulkin kasar nan a karo na biyu, amma abin mamaki sai a wannan mako ne ministocin nasa suka fito.
A lokacin da aka zabe shi a karo na farko a shekarar 2015 sai da ya kwashe wata shida kafin ya nada ministocin da zai yi aiki da su. A wancan lokacin ana ganin saboda shi sabo ne, dole yana bukatar lokaci sosai da zai yi nazari domin gudun kada a yi kitso da kwarkwata.
Sai dai kuma a wannan karo babu dalilin ba shi wannan uzuri domin ya riga ya zama dan gida tunda ya kwashe shekara hudu yana mulkin kasar nan, saboda haka mutane da dama sun dauka ana kammala rantsar da shi zai fito da sunayen ministocinsa domin a ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba, amma hakan bai yiwu ba. Hasali ma dai Shugaba Buhari bai fito da sunayen ministocinsa ba har sai da Majalisar Dattawa ta matsa masa, inda ta nuna masa cewa idan bai mika mata sunayen ministoci domin tantancewa zuwa karshen watan Yuli ba, za ta tafi hutunta na wata biyu da ta saba.
A sakamakon haka ne Shugaba Buhari ya mika mata sunayen ministoci guda 43 kuma nan da nan majalisa ta himmantu ta tantance su cikin kwana takwas.
Domin kammala tantancewar cikin hanzari, majalisa ta yi amfani da tsarin tsame duk wanda ya taba zama dan Majalisar Dattawa ko ta Wakilai daga amsa tambayoyi sai dai kawai ya yi gaisuwa ya fita. Haka kuma a wannan karo hatta wadanda suka taba zama ’yan majalisa a jihohi sun amfana da wannan karimci. Mata ma an karrama su an ce su yi gaisuwa kawai su fita.
Haka kuma saboda a kammala tantancewar da sauri, majalisa ta rika zama a ranakun Litinin da Juma’a kuma a kowace rana tana zama na fiye da awoyin da ta saba.
Mutane da dama sun dauka lokacin da Shugaba Buhari ya tafi Ingila ya yi makonni biyu yana hutawa bayan an kammala zabe, ya je ya kebe ne ya rubuta sunayen ministocin da zai yi aiki da su ta yadda ana kammala rantsar da shi zai fitar da sunayen, amma da ya dawo sai aka ji shiru, aka zauna sai dai jita-jita kawai ke yawo.
Da surutu ya yi yawa ne sai Shugaba Buhari ya bayyana cewa a wannan karon yana so ya nada mutanen da ya sani ne, maimakon a gwamnatinsa na karo na farko da ya yi amfani da bayanin mutanen da ya nada da ke rubuce.
Babu shakka yanzu kam ya nada mutanen da ya sani, domin ya dawo da tsofaffin ministoci 12 kuma ya nada shugabannin hukumomin Gwamnatin Tarayya da dama da ya yi aiki da su, kamar Dokta Isa Ali Pantami na Hukumar Kula da Harkar Ilimin Kwamfuta (NITDA) da Misis Sharon Ikeazor ta Hukumar Kula da Biyan Fansho (PTAD) da Sa’adiyya Umar Farouk ta Hukumar Yaki da Safarar Mutane da sauransu.
Haka kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya ba sabo ba ne, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Abba Kyari tsohon hannu ne, masu taimaka wa Shugaban Kasa ta fuskar yada labarai duk suna nan ba a canja su ba, kuma da dama daga cikin hadiman Shugaban Kasa duk suna nan.
Tun da yanzu ya nada mutanen da ya sani ya kamata ya himmatu wajen yi wa mutane aiki ba tare da bata lokaci ba, domin mutane suna cikin matsuwa suna bukatar a fito da abubuwan da za su saukaka musu. Kuma taimakon da suke bukata na gaggawa ne domin a takure suke a halin yanzu.
Ana cewa gaggawa babu kyau ko gaggawa daga Shaidan ne, to ba a kowane lokaci ne haka ke faruwa ba, akwai lokuta da dama da ake daukar matakan gaggawa domin a yi maganin matsalolin da suka taso.
Saboda haka akwai bukatar Shugaba Buhari ya kara wuta domin ya canja sunan da shi kansa ya fada da bakinsa cewa ana kiransa da shi, wato Baba mai tafiyar hawainiya (Baba go slow). Yanzu hanya ta bude sai a kara gudu domin a isa tudun- mun- tsira a kan lokaci.
Yanzu babu dalilin jan kafa, domin ’yan majalisa nasa ne, ministoci ’yan cikin gida ne, ba baki ba ne a gwamnatinsa, aiki kawai za su yi ba tare da bata lokacin yin wani nazari ba.
Ya kamata a mayar da tsofaffin ministoci ma’aikatunsu domin su ci gaba da ayyukan da suka fara, domin idan aka canja musu ma’aikatu sun koma sababbi ke nan sai sun dauki lokaci suna nazari kafin su fara aiki, alhali kuwa wannan lokaci na mataki na gaba da aka shiga na yin ayyukan da za su share wa talakawa hawaye da sauri ne ba lokaci ne na nuku-nuku ba. Su kuma sababbin a tura su ma’aikatun da suke da kwarewa yadda ba za su dade ba za su gane bakin zaren, kuma tunda fagensu ne aka tura su ba za a yi musu wala-wala ba.
Ya kamata Shugaba Buhari ya zama abin misali ne ga gwamnonin jihohi, maimakon gwamnoni su zama abin misali gare shi, domin gwamnoni da dama sun yi nisa wurin fara aiki ba tare da bata lokaci ba.