Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya a kan kada su biye wa manyan jam’iyyu biyu a kasar na APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023.
Tsohon Wakilin Shiyyar Kano ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, ya ce babu abin da manyan jam’iyyun biyu za su yi wa ’yan Najeriya tinkaho da shi da zai janyo ra’ayinsu domin zabensu a babban zaben kasa na badi da ke tafe.
- NAFDAC ta kama ganda mai dauke da guba ta N23m a Legas
- An kama mai shekaru 52 da dala miliyan 4.7 na jabu a Abuja
Wannan kalami na Kwankwaso da ke zaman babban jigo a jam’iyyar PDP na zuwa ne a yayin wani shiri da gidan Rediyon Nasara FM ya gabatar a ranar Asabar.
A cewarsa, manyan jam’iyyun biyu babu abin da suka tara face mahassadda, yana mai kiran ’yan Najeriya da cewa maimako su sake zabensu, su mai da hankalinsu kan wata jam’iyyar ta daban domin hakan ne kadai zai kai kasar nan zuwa tudun mun tsira.
“Ni ban ga wani abu da jamiyyar PDP ko APC za su yi wa ’yan Najeriya tinkaho da shi da zai janyo ra’ayinsu wajen sake zabensu a zaben 2023 da ke tafe,” a cewarsa.
A baya bayan nan dai ana ci gaba da alakanta Kwankwaso da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa wata jam’iyyar, lamarin da ke kara tsamin dangartaka tsakaninsa da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Kano.