✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansiloli sun tayar da tarzoma a ofishin APC

‘Yan takarar kansilan jam’iyyar APC sun yi barazanar kone ofisoshin jam’iyyar da ke adawa da juna a jihar Kuros Riba. ‘Yan takarar karkashin Effiom Yellow-Duke…

‘Yan takarar kansilan jam’iyyar APC sun yi barazanar kone ofisoshin jam’iyyar da ke adawa da juna a jihar Kuros Riba.

‘Yan takarar karkashin Effiom Yellow-Duke sun rufe ofisoshin bangarorin jam’iyyar, suka kuma yayyaga tutucin jam’iyyar.

Sun kuma lakada wa mutanen da suka riska a sakatariyar jam’iyyar na bangaren Etim John a garin Kalaba, babban birnin jihar.

Masu boren sun ce dole bangarorin jam’iyyar su hade su kuma shiga yunkurin zaman lafiya a jam’iyar, kuma duk sakatariyar bangaren da aka bude, to za su cinna masa wuta.

Sun ce ba za su lamunci duk wani take-take da ke nuna cewa kansu a rabe yake.

Masu zanga-zangar sun bayyana bacin rai cewa duk da gudunmuwar da suka bayar na kudi a zaben da ya gabata, an yi watsi da su.