Kansilan mazabar Vulpi da ke karamar hukumar Numan a jihar Adamawa, Wakana Enan Ngari wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin satar shanu da wasu laifuffuka ya mika kansa-da-kansa ga ‘yan sanda a garin Numan da ke jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin Yola.
Nguroje ya ce tuni aka garzaya da wanda ake zargin zuwa sashen binciken laifuffuka na rundunar ‘yan sandan saboda kaddamar da bincike.
- EFCC ta kama tsohon kansila kan zargin satar motoci
- An bindige tsohon kansila kan zargin leken asiri ga masu satar mutane
- Kansila ya tallafa wa mata da matasa a Legas
“Rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa tana sanar da al’umma cewa, shugaban mazabar Vulpi da ke karamar hukumar Numan ya mika kansa ga ‘yan sanda.
“Gwamnatin jihar Adamawa ta yi shelar neman shugaban mazabar ne bayan an zarge shi da taka rawa wurin aikata wasu laifuffuka.
“Ya mika kansa ga ‘yan sanda ne a garin Numan kuma tuni aka garzaya da shi zuwa sashen gudanar da binciken laifuffuka saboda kammala bincike.” In ji kakakin ‘yan sandan.
Nguroje ya kuma ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Olugbenga Adeyanju yana kira ga al’umman jihar da su kwantar da hankulansu.
Nguroje ya kara da cewa, shugaban ‘yan sandan ya bada tabbacin cewa za a hukunta mutumin idan har aka same shi da laifi inda ya jadadda cewa ‘yan sanda suna aiki tukuru saboda tabbatar da adalci ga kowa.