✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano za ta samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta – Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada kai da kasar Spain don samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta don farfado da…

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada kai da kasar Spain don samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta don farfado da masana’antu a jihar.
Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin sabbin zababbun Shugbannin Cibiyar Ciniki, Ma’adinai da Al’amuran Noma ta Jihar Kano (KACCIMA)  a gidan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa rashin tsayayyiyar wutar lantarki shi ne makasudin da ya jawo durkushewar masana’antu a jihar. “Sanin kowa ne sai da wutar lantarki harkokin kasuwanci, musamamn ma na masana’antu ke tafiya. Lamarin da ya jawo kusan dukkanin masana’antunmu suka durkushe a halin yanzu, babu shakka hakan ba karamin ci baya ba ne a harkar kasuwanci,” inji shi.
Ganduje ya hori shugabannin na KACCIMA da su yi kokari wajen ganin jihar ta ci gaba da rike kambunta na cibiyar kasuwanci.
A nasa jawabin sabon zababben Shugaban KACCIMA Alhaji Umar Faruk dansuleka ya bayyana cewa  za su yi kokarin dora kasuwannin jihar a bisa tsarin da zai ciyar da harkar kasuwanci gaba. “muna sane da yadda harkar kasuwanci ta tabarbare a jihar nan, hakan ya sa muke so mu dora kasuwanninmu a kan wani tsari da zai ciyar da harkar kasuwanci gaba wanda kuma zai zama ya yi daidai da yadda ake tafiyar da harkar kasuwanci a duniya,” inji shi.
A karshe shugaban ya yi kira ga sauran ’yan kasuwa da su bai wa cibiyarsu hadin kai don kai wa ga gaci.