✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano ta shirya tunkarar gasar tsalle-tsalle da guje-guje na lasa – Galadima

Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta bayyana cewa a shirye take tsaf don tunkarar gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje na lasa da za a fara…

Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta bayyana cewa a shirye take tsaf don tunkarar gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje na lasa da za a fara a watan Disamba mai zuwa a Abuja.

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima ne ya bayyana haka a ranar Asabar din da ta gabata a lokacin da yake karbar tawagar shugabannin shirya gasar wasannin wanda suka je don kunna wutar da ke alamta cewa za a gudanar da wasan a wannan shekara.

Ita dai wannan gasa an saba gudanar da ita ne a duk bayan shekaru bibbiyu sai dai zuwa yanzu an shafe shekaru shida ba a gudanar da ita ba saboda wasu dalilai da ba a ambata ba.

Alhaji Galadima ya ce hukumarsa ta riga ta kammala shirye-shirye game da dukkanin wasannin da Jihar Kano za ta shiga, inda a wannan wata ne za a fara horar da ’yan wasan da za su taka rawa a wasannin.

“A yanzu haka muna lolarin dawo da ’yan wasanmu da ke wajen Kano don fara daukar horo a wannan wata. Muna da ’yan wasa kimanin 280 wadanda za su taka rawa a wasanni 22 da Jihar Kano za ta shiga a lokacin gasar.”

Galadima ya bayyana cewa zuwan ’yan tawagar gwamnatin tarayyar ya nuna cewa gwamnatin da gaske take wajen dawo da wannan bikin tare da gudanar da shi a bana.

A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano tana bayar da dukkanin gudummawar gwargwadon larfinta game da harkar wasanni.

“Gwamnati tana bayar da gudummawarta sosai ga harkar wasanni kasancewa harka ce ta matasa wadanda su ne suka fi kowa yawa a cikin al’umma.

Game da rashin nasara da Lungiyar Kano Pillars ta yi a makon jiya a gasar cin kofin lalubale na lasa kuwa, Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa ’yan wasan lwallon Kano Pillars ba su yi nasara a wasannin ba, amma sakamakon rawar ganin da suka taka a wasan ya janyo an san ’yan wasan inda suka yi fice.

“Kowa ya san cewa ’yan wasanmu sun yi lolari yadda ya kamata, hakan ya jawo sun yi fice an san su. Na tabbata daga cikin ’yan wasanmu da suka yi wasa idan Allah Ya yarda za a samu wadanda za su buga wa Lungiyar Lwallon Lafa ta Super Eagles. kasancewar sun  taka muhimmiyar rawa a wannan lokaci.”

Har ila yau Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya yi kira ga ’yan wasan jihar da za su taka rawa a gasar wasannin da za a yi, da su yi lolarin lashe wa jihar kofuna kasancewar jihar ta yi fice a wasanni daban-daban a fadin lasar nan.