Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC) ta ce tuni ta fara shirye-shiryen gudanar da zabukan kananan hukumomi da ta tsara gudanarwa a shekara ta 2021.
Shugaban hukumar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da ya karbi bakuncin ’yan kwamitin zartarwa na hadakar jam’iyyu (IPAC) a ofishin hukumar.
Ya kuma ba su tabbacin yin aiki tare da dukkan jam’iyyun ba tare da nuna bambanci ba, kuma sun shirya tsaf domin ganin cewa ba a sake samun matsalar rashin kai kayan zabe a kan lokaci kamar yadda aka fuskanta ba a zaben 2018.
Sheka a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Dahiru Lawan Wambai ya fitar ya ce tuni shirye-shirye suka yi nisa wajen ganin an gudanar da zaben ba tare da tangarda ba.
A nasa jawabin, shugaban IPAC, Isa Nuhu Isa ya tabbatar wa KANSIEC ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya domin a samu sahihin zabe.
Idan za a iya tunawa, tun a watan Yulin da ya gabata Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin sauya fasalin shugabancin Jam’iyyar APC a Kananan Hukumomi 44 na Jihar a shirye-shiryen zaben da ke tafe.
Kakakinsa Abba Anwar a wata sanarwa a baya ya ce an kafa kwamitocin sasanta ’yan jam’iyyar da zai zagaya kowace mazaba a jihar domin kara karfafa jam’iyyar.