Gwamnatin jihar Kano ta bude shafin intanet da zai rika samar da bayanan cutar COVID-19 ga mutunen ciki da wajen jihar.
Jihar ta kirkiri shafin ne a matsayin kafar samar da labaru da bayanai game da cutar COVID-19 domin jama’a su fahimci yanayinta da illolinta cikin sauki.
Da yake gabatar da shafin ga Gwamna Abdullahi Ganduje a gidan gwamnatin jihar, Injiniya Mohammed Tahir, ya kara da cewa shafin “Zai kuma taimaka wa jami’an lafiya wajen tattara bayanai, ba a kan cutar coronavirus ba kadai , har ma sauran matsalolin rashin lafiya da ke addabar mutane”.
Masu coronavirus a Kano sun haura 1,000
Coronavirus: Matashi ya kirkiri na’urar wanke hannu a Kano
Mace-macen Kano: Sakamakon bincike sun yi karo da juna
Ya bayyana cewa bangarorin da shafin ya kunsa sun hada da na alkaluman wadanda suka kamu da cutar da kuma fam din wadanda ake zargin suna dauke da cutar, wadanda duk za a iya saukewa cikin sauki domin amfani da su idan bukatar hakan ta taso.
A bayaninsa, Gwamna Gaduje ya ce yanayin kulen da ake ciki da kuma karancin kudi sun sa ya zama dole a yi amfani da kimiya wajen magance cutar, yana mai cewa shafin zai saukaka wa mutanen sanin halin da jihar ke ciki a kan cutar.
Sai dai kuma ya nuna rashin jin dadi bias yadda ke kin bin ka’idojin kariya daga cutar sannan ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar mutane suna amfani amawalin fuska saboda muhimmacinsa.